Ekiti: Abokin Takarar Segun Oni Ya Fice Daga SDP, Ya Koma Jam'iyyar APC

Ekiti: Abokin Takarar Segun Oni Ya Fice Daga SDP, Ya Koma Jam'iyyar APC

  • Jam'iyyar SDP reshen jihar Ekiti ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta wanda ya tattara ya sauya sheƙa zuwa APC mai mulki
  • Ladi Owolabi, abokin gamin Segun Oni, ɗan takarar gwamna a inuwar SDP a zaben da ya gabata, ya fice daga jam'iyyar zuwa APC
  • Ya samu kyakkyawar tarba daga shugaban jam'iyya na gundumarsa a Ado-Ekiti, babban birnin jihar kuma ya ɗauki alƙawari

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ekiti - Ɗan takarar mataimakin gwamna karkashin inuwar jam'iyyar SDP a zaben da ya gabata a jihar Ekiti, Ladi Owolabi, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC

Jaridar Tribune a Najeriya ta rahoto cewa Mista Owolabi ya tabbatar da shiga APC ne a gundumarsa da ke Ado Ekiti, babban birnin jihar ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba.

Ladi Owolayi da Segun Oni.
Ekiti: Abokin Takarar Segun Oni Ya Fice Daga SDP, Ya Koma Jam'iyyar APC Hoto: Facebook
Asali: UGC

Owolabi ya samu tarba hannu bibbiyu daga shugaban APC na gundumarsa, Ojo Adeyanju, tare da wasu mambobin jam'iyyar kuma ya nuna jin daɗi bisa yadda aka karɓe shi.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wani Babban Likita Da Ake Ji Da Shi a Jihar Arewa

Ya bayyana cewa shi masoyin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne kuma yana ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar magoya bayan Tinubu (SWAGA) duk da a lokacin yana ƙarƙashin tsohon uban gidansa, Cif Oni.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Owolabi ya ce:

“Idan har wasunku sun san tafiyata a siyasa, ba za ku iya cewa tun farko na bar APC ba, ni dan kungiyar SWAGA ne, kuma ina ganin duk kun san abin da kungiyar ta ke nufi."
"Ko a lokacin zaben gwamnan da ya gabata, fada ne mai tsanani, kuma a lokaci guda, na ci gaba da zama mamban SWAGA mai kishin kasa, don haka na kasance ɗan gida a APC."

Owolabi ya yaba wa gwamna Oyebanji

Owolabi ya kuma yaba wa Gwamna Biodun Oyebanji na Ekiti kan ayyukan da ya zuba wa al'umma, inda ya ce shi ne ya taka muhimmiyar rawa wajen sauya sheƙa zuwa APC.

Kara karanta wannan

Akpabio Na Cikin Matsala Yayin Da Shirin Tsige Shi Ke Kara Karfi, Bayanai Sun Fito

Tsohon jigon na SDP ya jaddada mubaya'a ga APC, ya kuma sha alwashin taimakawa wajen samun nasara a yunkurin tabbatar da ajandar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Mutfwang Ya Maida Martani Kan Hukuncin da Kotu Ta Yanke a Filato

A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Filato ya nuna farin ciki bisa nasarar da ya samu kan APC a kotun sauraron ƙararrakin zabe mai zama a Jos.

Celeb Mutfwang ya ce koken da jam'iyyar APC ke gabatarwa a gaban Kotun ɓata lokaci ne kawai amma sun san gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel