Tashin Hankali Yayin da Prophet Elijah Ya Yi Hasashen Kama Peter Obi Gabannin Shiga Kotun Koli

Tashin Hankali Yayin da Prophet Elijah Ya Yi Hasashen Kama Peter Obi Gabannin Shiga Kotun Koli

  • Shugaban cocin Glorious Mount of Possibility, Prophet David Elijah, ya yi kira ga magoya bayan Peter Obi da su yi wa dan takararsu addu'a
  • Prophet Elijah ya yi hasashen cewa za a kama Peter Obi, dan takarar jam'iyyar Labour Party a zaben shugaban kasa na 2023 nan ba da dadewa ba
  • Malamin addinin ya yi hasashen ne yayin da tsohon gwamnan na jihar Anambra ke shirin fara shari'arsa a kotun koli kan hukuncin kotun zaben shugaban kasa

Ikeja, Lagos - Wani malamin addini mazaunin jihar Lagas, Prophet David Kingleo Elijah na cocin Glorious Mount of Possibility, ya haddasa fargaba yayin da ya yi hasashen cewa za a kama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi.

A wani hasashe da ya yi a bidiyo a shafinsa na Youtube, malamin addinin ya yi kira ga magoya bayan tsohon gwamnan na jihar Anambra da su taya dan takararsu da addu'a don kada a tsare shi.

Kara karanta wannan

Yadda Likita Ya Yanke Jiki Ya Mutu Bayan Ya Shafe Tsawon Awanni 72 Yana Aiki a Asibitin LUTH

Malamin addini ya yi hasashen kama Peter Obi
Tashin Hankali Yayin da Prophet Elijah Ya Yi Hasashen Kama Peter Obi Gabannin Shiga Kotun Koli Hoto: Peter Obi
Asali: Twitter

Prophet Elijah ya yi hasashen kama Peter Obi

"Kamu wata matsa ce. Sai kun yi wa dan uwanku, dan takararku, Peter Obi addu'a. Ku yi masa addu'a, saboda ban san me wannan kamun ke nufi ba. Menene laifinsa? Menene matsalar ma? Ban sani ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Nawa dai shine addu'an zaman lafiya. Nawa shine na yi addu'an soyayya. Nawa shine na yi addu'an hadin kai."

Peter Obi ya garzaya kotun koli kan hukuncin kotun zaben shugaban kasa

Hasashen malamin na zuwa ne gabannin shirye-shiryen da Obi ke yi na daukaka kara a kotun koli kan hukuncin da kotun zaben shugaban kasa ta yanke.

Obi, wanda ya zo na uku a zaben shugaban kasa na 2023, ya kalubalanci sakamakon zaben ranar 25 ga watan Fabrairu a gaban kotun zaben. Sai dai kuma an soke kararsa saboda rashin hujja.

Kara karanta wannan

Elon Musk Ya Bayyana Shirin Fara Biyan Kudi Duk Wata Ga Masu Amfani Da Twitter, Ya Bayyana Dalili

Obi da Labour Party sun yi watsi da hukuncin sannan sun daukaka kara a gaban kotun koli, yana mai neman babbar kotun ta soke nasarar shugaban kasa Bola Tinubu da jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kalli bidiyon a kasa:

Malamin addini ya gargadi Atiku da Obi, ya ce guguwar sauya sheka na nan tafe Ga LP da PDP

A wani labarin, munnji cewa jagoran majami'ar INRI, Primate Elijah Ayodele, ya roƙi Peter Obi da Atiku Abubakar su hanzarta su, "Koma gida su gyara wurin da ya cukurkuɗe."

Mista Obi ne ya riƙe tutar takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar LP yayin da Atiku ya nemi zama shugaban ƙasa a babban zaben 2023 a inuwar jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel