Kotu: Dole Mu Hada Karfi Mu Tafi Tare a Cikin Wannan Yanayin, Abba Gida-Gida

Kotu: Dole Mu Hada Karfi Mu Tafi Tare a Cikin Wannan Yanayin, Abba Gida-Gida

  • Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya bai wa kwamishinoni da hadiman da ya naɗa shawara bayan Kotu ta sauke shi
  • Abba ya buƙaci su bar komai a hannun Allah kuma har yanzun yana da damar ɗaukaka ƙara zuwa Kotun sama
  • A cewarsa, har yanzu jama'a a kananan hukumomin jihar Kano 44 suna tare da gwamnatinsa kuma suna mata addu'a

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bukaci muƙarrabansa da ya naɗa a muƙamai daban-daban su haɗa kai su tunkari guguwar da ta taso.

Abba Gida-Gida ya bayyana haka ne yayin wani taro da ya kira na dukkan muƙarrabansa awanni bayan Kotun zaɓe gwamnan jihar Kano ta soke nasarar NNPP.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.
Kotu: Dole Mu Hada Karfi Mu Tafi Tare a Cikin Wannan Yanayin, Abba Gida-Gida Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Kotun sauraron ƙarar zaben gwamnan ta tsige Abba kuma ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Mataimakin Gwamna Ya Taro Faɗan da Ya Fi Ƙarfinsa, Ya Roƙi Gwamnan PDP Ya Yafe Masa

Abinda Abba Gida-Gida ya faɗa wa hadimansa

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa da yake maida martani kan hukuncin, gwamnan ya bukaci wadanda ya naɗa a gwamnatinsa su miƙa lamurransu baki ɗaya ga Allah (SWT).

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma faɗa musu cewa har yanzu gwamnatinsa tana da damar ɗaukaka ƙara zuwa gaba dangane da hukuncin da Kotu ta yanke a jiya Laraba.

Abba Gida-Gida ya ce:

"Idan kai kwamishina ne, ko mai ba da shawara ko MD, menene abin da ke ƙarƙashinka a ofis? Dole ne jagora ya tsaya tsayin daka, ku bar komai a hannun Allah Madaukakin Sarki, ya ishe mu, kuma bai yarda da zalunci ba."
"Ya zama wajibi mu zama masu ƙarfin zuciya, mu tunkari kowane hazo ya taso. Ya kamata mu ci gaba da fadakar da jama'a cewa wasan bai ƙare ba, zamu ɗaukaka ƙara zuwa Kotun gaba."

Kara karanta wannan

Nasiru Gawuna Ya Tika Rawa Bayan Nasara Kan Gwamna Abba a Kotu? Gaskiya Ta Bayyana

“Gwamnati na da isasshen lokacin da za ta yiwa al’ummar jihar Kano hidima, manufofinmu na nan, mun ɗauki alkawari kuma da ikon Allah mun fara aiwatar da tsare-tsaren mu."

Gwamnan ya ƙara da cewa duk da hukuncin da Kotu ta yanke, mazauna kananan hukumomin Kano 44 suna musu addu'a da fatan nasara, rahoton Naija News ya tattaro.

Tsohon Gwamnan Jihar Katsina Na PDP Ya Bayyana Dalilinsa Na Yaƙar Atiku a Zaben 2023

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan Katsina ya bayyana cewa Atiku ne ya jawo wa kansa matsala a zaben shugaban ƙasa na 2023.

Ibrahim Shema, ya ce yadda aka nuna masa ba shi da amfani anwurin kamfe ne ya sa ya koma ya haɗa kai da jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel