Jogin Jam’iyyar NNPP, Abbas Ya Zargi Kwankwaso Kan Rasa Kujerar Gwamna a Jihar Kano

Jogin Jam’iyyar NNPP, Abbas Ya Zargi Kwankwaso Kan Rasa Kujerar Gwamna a Jihar Kano

  • Wani jigon jam'iyyar NNPP, Alhaji Abbas ya zargi Rabiu Kwankwaso kan rashin nasarar jam'iyyar a jihar Kano
  • Abbas ya bayyana haka ne a yau Alhamis 21 ga watan Satumba a cikin wata sanarwa da ya fitar
  • Ya ce son rai irin na Kwankwaso da kuma neman mukamin minista shi ya jawo musu hakan a jihar Kano

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Jigo a jam’iyyar NNPP, Alhaji Abbas Onilewura ya zargi dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso kan rasa nasarar jam’iyyar a jihar Kano.

A jiya Laraba 20 ga watan Satumba kotun ta yanke hukunci inda ta tsige Gwamna Abba Kabir na jam’iyyar a matsayin gwamna, Leadership ta tattaro.

An zargi Kwankwaso da kawo rashin nasarar NNPP a Kano
Jogin Jam’iyyar NNPP Ya Zargi Kwankwaso Kan Rasa Kujerar Gwamna a Kano. Hoto: Abdullahi Ganduje, Rabiu Kwankwaso.
Asali: Facebook

Meye ake zargin Kwankwaso a kai a Kano?

Kotun har ila yau, ta tabbatar da Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaban APC Ya Jagoranci Murnar Nasara A Kotun Zaben Kano, Bayanai Sun Fito

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin da ya ke martani kan hukuncin, Abbas ya ce Kwankwaso ya siyar da jam’iyyar lokacin da ya ke tattaunawa da APC kan mukamin minista a Abuja.

Onilewura ya bayyana haka ne a yau Alhamis 21 ga watan Satumba a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce zagon kasa da Kwankwaso ya yi wa jam’iyyar ce ya jawo rashin nasararta a hukuncin kotun da aka yanke a jiya.

Meye martanin NNPP ga Kwankwaso a Kano?

Ya ce:

“Wannan rashin nasara babbar asara ce a jam’iyyar mu kuma hakan ya faru ne saboda son rai na Kwankwaso wanda ya siyar da jam’iyyar.
“Yayin da mu ke jiran sahihin kwafi na hukuncin kotun, muna sanar da cewa hakan ba zai faru ba idan da Kwankwaso ya bi ka’ida na bai wa wanda ya dace tikitin takara.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Tsige Abba Gida-Gida Daga Kujerar Gwamnan Kano, Ta Faɗi Wanda Ya Ci Zaɓe

“Binciken mu ya tabbatar cewa yadda Kwankwaso ya ke bin APC a gindi shi ya jawo su ka yi amfani da rauninshi wurin kwace kujerar.”

Ya kara da cewa abin bakin ciki ne yadda su ka gama shan wahala kawai lokaci guda Kwankwaso ya zo ya mayar da wahalarsu ta banza.

Abbas ya gargadi Kwankwaso da ya yi nesa da shiga cikin lamuran jam'iyyar NNPP a ko wane mataki.

Kwankwaso ya yi martani kan hukuncin zabe a Kano

A wani labarin, tsohon kwamishina a Kano, Dakta Ilyasu Kwankwaso ya shawarci Abba Kabir da ya karbi hukuncin kotu da zuciya daya.

Kwankwaso ya ba da shawarar ce bayan kotu ta yanke hukunci tare da kwace kujerar Abba Kabir.

Asali: Legit.ng

Online view pixel