Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Shaibu Ya Bai Wa Obaseki Hakuri

Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Shaibu Ya Bai Wa Obaseki Hakuri

  • Mataimakin gwamnan jihar Edo ya ce yana kewar kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninsa da gwamna Godwin Obaseki
  • Philip Shaibu ya roƙi ubangidan nasa watau gwamna Obaseki ya yafe masa idan ya masa wani abu da ba daidai ba
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnan ya fitar da Shaibu daga ofishinsa na gidan gwamnati a Benin

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo da ke cikin ruɗani, Mista Philip Shaibu, ya fara yunƙurin neman sulhu da mai gidansa, gwamna Godwin Obaseki.

Philip Shaibu, ya roki shugabansa, Gwamna Godwin Obakeki na jam'iyyar PDP, ya yafe masa kura-kuran da ya yi bisa sabanin siyasar da ya shiga tsakaninsu.

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu.
Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Shaibu Ya Bai Wa Obaseki Hakuri Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Mataimakin gwamnan ya faɗi haka ne yayin wata hira da 'yan jarida da ke gudana yanzu haka a gidansa da ke Benin City, babban birnin jihar Edo, yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida-Gida Ya Faɗa Wa Kwamishinoni da Hadimai Magana Mai Jan Hankali Bayan Kotu Ta Tsige Shi

Shaibu ya buƙaci gwamna Obaseki ya yafe masa kuma ya manta da duk saɓanin da ya faru a tsakaninsu, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaibu ya ce:

“Kamar yadda na sha faɗa, ni bawa ne mai biyayya kuma babu abin da ya canza. Na dauki alkawarin goyon bayan gwamna kuma kamar yadda kuke gani mabiya darikar Katolika sun zo nan."
“Ni idan na ɗauki alkawari da Allah, babu wani abu da zai canza shi. Ina fatan cewa dangantakar da muke da ita a baya ta dawo, na yi addu'a kuma na san cewa nan da makonni masu zuwa za ta dawo."
“Na yi kewar gwamna kuma ina ta addu’a Allah ya sanyaya zuciyar gwamna da dukkan mu, har ma wadanda suke kokarin shiga tsakaninmu, Allah ya taba zukatansu su san cewa alheri nake nufi."

Kara karanta wannan

Rikici: Magana Ta Ƙare, Gwamnan PDP Ya Ƙori Mataimakin Gwamna Daga Gidan Gwamnati, Sanarwa Ta Fito

Shaibu ya aike da saƙo ga Obaseki

Shaibu ya ce saura shekara guda ta rage musu shi da gwamnan, kuma sun kasance masu kishin kasa baki ɗaya saboda da dama suna ganin hakan ba zai yiwu ba.

Daily Trust ta rahoto mataimakin gwamnan na cewa:

"Don haka, mai girma gwamna idan akwai wani abu da ka ji na yi don Allah ka yi hakuri, ina bukatar mu hada kai domin mu kammala mulki lafiya, addu'ata kenan a gare ka."

Yan Sanda da Jami'an Lafiya Sun Tono Gawar Mawaki Mohbad Daga Kabari

A wani rahoton kun ji cewa 'Yan sanda da jami'an lafiya tona ƙabarin fitaccen Mawakin nan Mohbad, sun ciro gawarsa domin gudanar da bincike.

Ilerioluwa Aloba wanda aka fi sani da Mohbad ya mutu ne ranar 12 ga watan Satumba, 2023 kuma aka ɓinne shi washe gari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel