Enugu: Kotun Zabe Ta Kori Karar da Aka Zargi Gwamna Mbah da Takadar NYSC Ta Bogi

Enugu: Kotun Zabe Ta Kori Karar da Aka Zargi Gwamna Mbah da Takadar NYSC Ta Bogi

  • Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamnan ta sanar da hukuncinta kan zargin da ake wa gwamnan Enugu na amfani da takardar NYSC ta jabu
  • Da take yanke hukunci ranar Alhamis, Kotun ta ce wanda ke ƙara ya gaza gamsar da ita da kwararan hujjoji
  • Bugu da ƙari, Kotun ta kori ƙarar nan take wacce ɗan takarar gwamna a inuwar PRP, Christopher Agu ya shigar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Enugu - Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna ta yi watsi da ƙarar da ake tuhumar Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu da amfani da takardar shaidar aikin yi wa kasa hidima (NYSC) ta jabu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ɗan takarar gwamnan jihar a inuwar jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Christopher Agu, ne ya shigar da ƙarar gaban Kotu.

Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah.
Enugu: Kotun Zabe Ta Kori Karar da Aka Zargi Gwamna Mbah da Takadar NYSC Ta Bogi Hoto: Peter Mbah
Asali: Twitter

Mista Agu ya yi zargin cewa Gwamna Mbah, wanda ya lashe zaben jihar Enugu ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, yana amfani da Satifiket ɗin NYSC na bogi.

Kara karanta wannan

Gawuna Ya Yi Magana Kan Nasarar Da Ya Samu a Kotu, Ya Aike Da Sako Mai Muhimmanci Ga Gwamna Abba Kabir Yusuf

Yadda Kotu ta yanke hukuncin kan ƙorafin PRP

Amma da take yanke hukunci ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba, Kotun zaɓe karkashin jagorancin mai shari'a Kudirat Morayo Akano, ta ce ƙarar ba ta cancanta ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ɗan takarar gwamna a inuwar PRP ya kuma yi zargin cewa Gwamna Mbah na PDP ya samu nasara a zaben ne sakamakon kura-kuran da aka tafka da kuma aringizon ƙuri'u.

Bisa waɗannan dalilai da ya zayyano a gaban Kotu, Mista Agu ta hannun lauyansa ya roƙi Kotu da ta rushe nasarar jam'iyyar PDP a zaben ranar 18 ga watan Maris.

Amma mai shari'a Akano, a hukuncin da ta karanto, ta riƙe cewa mai shigar da ƙara ya gaza gamsar da Kotu da kwararam hujjoji kan tuhumar da yake wa wanda ake ƙara.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Ganduje, Gawuna Suka Yi Murna Bayan Kotu Ta Tsige Abba Ya Yadu

Ta ce bangaren mai ƙara ba su gamsar da Kotu ba dangane da tuhume-tuhumen da suke wa Gwamna Mbah cewa ya yi maguɗi da damfara a zaɓen da ya gabata ba.

Kotun ta ce babu wata shaida da ke gabanta da ke tabbatar da ikirarin PRP na cewa an mika takardar shaidar NYSC ta jabu ga INEC.

Ta bayyana cewa, don tabbatar da jabun, ya kamata mai ƙara ya gabatar da takardar asali da kuma wacce yake zargin ta jabu ce.

Daga ƙarshe, Ƙotu ta tabbatar nasarar Gwamna Peter Mbah na jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Enugu da ya gabata, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Sanatan APC Ya Nada Sabbin Hadimai 100

A wani rahoton kuma Sanatan Ondo ta kudu ya naɗa sabbin masu taimaka masa na musamman 100 'yan asalin mazaɓarsa.

Dakta Ibrahim ya kuma sanar da cewa kowane mutum ɗaya daga cikin mutanen mazaɓarsa 100 da ya naɗa a matsayin masu taimaka masa zai samu tallafin N300,000.

Kara karanta wannan

"Akwai Kura-Kurai": Gwamna Abba Ya Magantu Kan Hukuncin Kotu, Ya Bayyana Mataki Na Gaba Da Zai Dauka

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel