Katsina: Shema Ya Bayyana Abinda Ya Sa Ya Yaki Atiku da PDP a Zaben 2023

Katsina: Shema Ya Bayyana Abinda Ya Sa Ya Yaki Atiku da PDP a Zaben 2023

  • Tsohon gwamnan Katsina ya bayyana cewa Atiku ne ya jawo wa kansa matsala a zaben shugaban ƙasa na 2023
  • Ibrahim Shema, ya ce yadda aka nuna masa ba shi da amfani a wurin kamfe ne ya sa ya koma ya haɗa kai da jam'iyyar APC
  • Wani jigon PDP da ke ƙaunar Shema ya ce a zahirin gaskiya irin wannan matsalolin suka jawo wa Atiku faɗuwa a 2023

Jihar Katsina - Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema, ya bayyana dalilan da suka sanya ya yaƙi ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar a zaben 2023.

Shema ya ce ya yaƙi Atiku da PDP a babban zaɓen 2023 saboda sun ɗauke shi a matsayin wanda bai da amfani kuma bai da tasiri, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Yanke Hukunci a Kotunan Zabe, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema.
Katsina: Shema Ya Bayyana Abinda Ya Sa Ya Yaki Atiku da PDP a Zaben 2023 Hoto: Ibrahim Shehu Shema
Asali: UGC

Shugaban tawagar midiya na tsohon gwamnan Katsina, Olawale Oluwabusola, ne ya bayyana hakan a wata makala da ya fitar ta murnar cikar Shema shekaru 66 a duniya, ranar Laraba.

Mista Oluwabusola ya ce tsohon gwamnan wanda ya bauta wa PDP tun da aka kafa ta, kuma bai taba guje mata ba sai a 2023 lokacin da ya yi wa APC kamfe a Katsina.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shema ya yanke shawarar yaƙar jam'iyyarsa ta PDP a jihar Katsina bisa muradi da sha'awar ɗaukacin al'ummar jihar, in ji Oluwabusola.

Hadimin tsohon gwamnan ya ce:

“A lokacin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP a 2023, Atiku ya mayar da Shema baya a lokacin ya zo kamfe Katsina, ya manta da cewa kowace siyasa daga tushe ake ɗauko ta."
"Shema ya dawo Katsina tun da wuri domin shirye-shiryen kamfen Atiku, amma daga baya ya tsame hannunsa saboda ya ga wani rubutu cewa ba a buƙatar aikinsa, da shi da babu duk ɗaya."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa Ya Maida Martani Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a 2023

"Tsohon mataimaƙin shugaban ƙasan ya yi kamfe da nasarorin PDP a lokacin mulkin Shema, ciki harda wurin da aka yi taron watau filin Karkanda, amma duk da haka ya gaza ambatar sunan Shema."

Oluwabusola ya ce watsin da Atiku ya yi da Shema lokacin kamfe shi ne ya jawo wa jam'iyyar PDP faɗuwa warwas a zaben shugaban ƙasa da na gwamna a Katsina, jaridar Headlines ta tattaro.

Kabir Abdullahi, wani jigon PDP a Katsina da ke goyon bayan Shema, ya shaida wa Legit Hausa cewa kwata-kwata ba a yi wa tsohon gwamnan adalci ba a lokacin yaƙin neman zabe.

A cewarsa, ya zabi PDP tun daga sama har ƙasa amma yana da yaƙinin cewa da wuya jam'iyyar ta kai labari saboda matsalolin cikin gida.

Ya ce:

"Babban abinda ya jawo wa 'yan takarar PDP musamman Atiku faɗuwa a zaɓe shi ne rashin jawo kowa a jiki, kusan kowace jiha zaka ga jam'iyyar nan ta rabu 2 kafin zaɓe."

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida-Gida Ya Faɗa Wa Kwamishinoni da Hadimai Magana Mai Jan Hankali Bayan Kotu Ta Tsige Shi

'Kowa ya san ƙarfin kuri'un Katsina, amma Atiku ya yi watsi da Shema, wanda indai za a faɗi waɗanda suka gina PDP a Katsina dole a sanya shi, to ka duba yadda aka lalata ƙuri'un, dole a gyara."

Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Shaibu Ya Bai Wa Obaseki Hakuri

A wani rahoton na daban Mataimakin gwamnan jihar Edo ya roƙi gwamna Obaseki ya yafe masa bisa saɓanin siyasar da ya shiga tsakaninsu.

Mataimakin gwamnan ya faɗi haka ne yayin wata hira da ya yida 'yan jarida a gidansa da ke Benin City, babban birnin jihar Edo, ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel