Magoya Bayan Jam’iyyar APC Sun Jefi Ganduje Da Ruwan Leda A Jihar Oyo Kan Zargin Zagon Kasa

Magoya Bayan Jam’iyyar APC Sun Jefi Ganduje Da Ruwan Leda A Jihar Oyo Kan Zargin Zagon Kasa

  • Rahotanni da ke samun mu sun tabbatar da cewa an jefi shugaban jam’iyyar APC ta kasa da ruwan leda a jihar Oyo
  • Abdullahi Ganduje ya gamu da fushin magoya bayan dan takarar gwamna a jihar na APC, Sanata Teslim Folarin kan zargin zagon kasa
  • Wannan lamari ya faru ne bayan Abdullahi Ganduje ya kamala jawabi ga shugabanni da kuma magoya bayan jam’iyyar a jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Oyo – Rahotanni sun tabbatar cewa an kai farmaki ga tawagar shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje yayin ziyara a jihar Oyo.

Legit ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a sakatariyar jam’iyyar a birnin Ibadan inda Ganduje ya yi jawabi ga ‘yan jam’iyyar.

Shugaban APC, Ganduje ya sha jifa a jihar Oyo
Magoya Bayan Jam’iyyar APC a Jihar Oyo Na Zargin Ganduje Da Zagon Kasa. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Meye ya jawo 'yan APC jifan Ganduje?

Yayin jawabin, Ganduje ya yi wa magoyan bayan jam’iyar da shugabanninta alkawarin samun nasara tun daga tushe har zuwa matakin kasa.

Kara karanta wannan

Akpabio Na Cikin Matsala Yayin Da Shirin Tsige Shi Ke Kara Karfi, Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma yabawa magoya bayan jam’iyyar wurin tabbatar da nasarar shugaban kasa, Bola Tinubu a zaben da ya gabata.

The Guardian ta tattaro cewa bayan kamala jawabin, fusatattun matasa sun jefi Gwanduje da ruwan leda saboda zargin wariya da zagon kasa ga jam'iyyar.

Su waye su ka jefi shugaban APC, Ganduje?

Fusatattun matasan ana hasashen magoya bayan dan takarar jam’iyyar APC ne, Sanata Teslim Folarin inda su ke zargin Ganduje da yi wa Gwamna Seyi Makinda na jam’iyyar PDP aiki.

An zabi Dakta Abdullahi Ganduje ne a matsayin shugaban jam’iyyar ta kasa bayan murabus na tsohon shugabanta, Sanata Abdullahi Adamu.

Rahotanni sun ruwaito cewa Sanata Adamu ya yi murabus ne kan zargin wasu na hannun daman shugaban kasa, Bola Tinubu sun saka shi a gaba bayan cin nasarar jam’iyyar.

Wannan na zuwa ne bayan wasu na zargin hakan bai rasa nasaba da goyon bayan Sanata Ahmed Lawan da tsohon shugaban APC ya yi lokacin zaben fidda gwani a Abuja.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Yi Babban Rashin Jigo, Sanata Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

Ganduje ya kafa kwamitin yakin neman zabe a jihar Imo

A wani labarin, shugaban jam’iyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kafa kwamitin kamfe na zaben gwamnan jihar Imo.

Ganduje ya yi wa Gwamna Hope Uzodinma alkawarin ba shi duk wata goyon baya da ya ke bukata a zaben.

Ya sha alwashin za su yi nasara a zabukan jihohin Imo da Kogi a watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel