Zaben Gwamnan Imo: Ganduje Ya Bayyana Abun Da Za Su Yi Don Yin Nasara

Zaben Gwamnan Imo: Ganduje Ya Bayyana Abun Da Za Su Yi Don Yin Nasara

  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya kaddamar da hedkwatar zaben jam'iyyar APC na zaben gwamnan jihar Imo
  • Ganduje ya bukaci mambobin jam'iyyar da su yi aiki dare da rana domin su lashe zaben da ke tafe a watan Nuwamba
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ba 'ya'yan jam'iyyar mai mulkin tabbacin yin nasara a zaben

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Imo - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Ganduje, ya yi kira ga mambobin jam'iyyar a Imo da su yi aiki dare da rana don lashe zaben gwamnan jihar da ke tafe a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Ganduje ya roki mambobin jam'iyyar ne yayin da yake kaddamar da hedkwatar kamfen din APC da ke hanyar Wethedral da ke Owerri a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Sabon Tsari: Jam'iyyar APC Ta Fara Tattara Bayanan 'Yan Najeriya Miliyan 40 Ta Intanet, Bayanai Sun Fito

Ganduje ya ce APC za ta lashe zaben gwamnan jihar Imo
Zaben Gwamnan Imo: Ganduje Ya Bayyana Abun Da Za Su Yi Don Yin Nasara Hoto: thenationonline
Asali: UGC

APC za ta lashe zaben gwamnan Imo, Ganduje ya ba da tabbaci

Ya ba mambobin jam'iyyar tabbacin cewa hedkwatar APC za ta zama wajen da za a samar da duk wasu dabaru don jam'iyyar ta yi nasara a zaben gwamnan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam'iyyar ya ce:

“Na yi mamaki. A yayin da nake kallon wannan katafaren ginin da ke nuni da cewa zaben gwamnan mai zuwa zai kasance babbar nasara da ke zuwa a jihar Imo.
"Wannan hadadden gini na musamman saboda zaben da kamfen ne kuma zai zama harabar da za a yi duk wasu tsare-tsare, inda za a shirya duk wasu dabaru.
"Wannan ya kasance don cin zaben ne. Mun yarda cewa za a ci wannan zabe. Gaba daya shugabannin kananan hukumomi, shugabannin jam'iyya na kananan hukumomi, dukkan masu ruwa da tsaki wannan ginin don sake ba ku tabbacin cewa za a yi nasara a zaben ne. Saboda haka ina mai kira gare ku da ku yi aiki dare da rana don mu yarda nasara yana gare mu."

Kara karanta wannan

Wole Soyinka Ya Tonawa Obidient Asiri, Sun San Peter Obi Bai Doke Tinubu ba

Ina barar kuri'unku don zarcewa kan kujerata, Gwamna Hope Uzodimma ga al'ummar Imo

Jaridar The Nation ta rahoto cewa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda ke neman zarcewa ya ce:

"Ya ku mutanena na jihar Imo, kamar yadda nake yawan fadi, wannan tafiyar ta fi gaban bangaranci da akidar jam'iyya, maimakon haka, wani hadin gwiwa ne kan nasarorin da aka samu. na gwamnatina a cikin shekarun da suka gabata, bayan farfado da jihar daga halin da take ciki.
"Ba zan iya tafiyar nan ni kadai ba, kuri'unlu na dogara da su a shekaru hudun farko kuma kuri'unku nake nema a shekaru hudu masu zuwa. A tare, mun farfado da jiharmu mai albarka, mun gyara cibiyoyinmu sannan sun sake gina ababen more rayuwarmu.
"Yanzu lokaci ya yi da za mu shiga mataki na gaba, inda gyare-gyare da manufofin da muka kafa za su taka muhimmiyar rawa wajen bunkasar tattalin arzikinmu da kwanciyar hankali domin amfanin kowa."

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Jihar Imo Na 2023: Malamin Addini Ya Bayyana Wanda Zai Yi Nasara

Ganduje, Gwamnonin APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Dira Jihar Imo

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, wasu gwamnoni da mataimakin kakakin majalisar wakilai, sun dira Owerri, babban birnin jihar Imo.

Manyan ƙusoshin jam'iyyar APC na ƙasa sun mamaye Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya ranar Jumu'a domin kaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel