Sanatan Jam'iyyar PDP a Jihar Edo, Mathew Urhoghide Ya Sake Koma Wa APC

Sanatan Jam'iyyar PDP a Jihar Edo, Mathew Urhoghide Ya Sake Koma Wa APC

  • Tsohon ɗan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Mathew Urhoghide, ya sake koma wa jam'iyyar APC
  • Sanata Urhoghide ya tattara kayansa ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC ne ranar Litinin, 18 ga watan Satumba, 2023
  • Tsohon sanatan ya zauna a majalisar dattawan Najeriya na tsawon shekaru takwas tsakanin 2015 zuwa 2023 yana wakiltar mazaɓar Edo ta kudu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benin, Jihar Edo - Tsohon sanatan mazaɓar Edo ta kudu a inuwar jam'iyyar PDP, Sanata Mathew Urhoghide, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Sanata Urhoghide ya tabbatar da koma wa jam'iyyar APC ne ranar Litinin, 18 ga watan Satumba, 2023, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Sanata Mathew ya koma APC.
Sanatan Jam'iyyar PDP a Jihar Edo Ya Sake Koma Wa Jam'iyyar APC Hoto: @efewonyi
Asali: Twitter

Wannan mataki ya zo ke kusan watanni huɗu bayan Sanatan ya yi murabus daga kasancewa mamba a jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Shugaban APC Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Bayan Lakaɗa Wa Kwamishinar Mata Duka a Wurin Rabon Tallafi

Meyasa Urhoghide ya zaɓi koma wa APC?

Ya samu tarba mai kyau daga shugaban APC na guduma, Mista Sunny Omokaro, a sakatariyar APC ta gunduma ta biyu da ke kan titin filin jirgin sama a Benin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake jawabi, Sanatan ya ce ya yi matuƙar farin cikin sake komawarsa gida watau jam'iyyar APC.

Urhoghide ya ƙara da cewa ko a baya ya bar jam'iyyar zuwa PDP ne saboda saɓanin da aka samu kan wasu batutuwa.

A kalamansa, tsohon sanatan ya ce:

“Lokacin da na yi murabus daga jam'iyyar PDP a watan Mayu, na ce zan koma wata jam’iyyar siyasa, muddin na ci gaba da kasancewa a cikin siyasa."
"Bayan na yi nazari sosai kan abubuwan da ke faruwa a Jihar Edo, sai na yanke shawarar komawa jam’iyyar da dani aka gina ta. Ni dan APC ne, nan ne nake da abokai na siyasa. Na zo ne domin mu sake gina APC."

Kara karanta wannan

Kotu Ta Soke Zaben Dan Majalisar APC, Ta Ba INEC Umarnin Sake Zabe

“Ba ni kadai na dawo APC ba, na taho tare da dimbin magoya bayana. Babu wata gunduma a ɗaukacin gundumomi 77 da ke yankin Edo ta Kudu da ban yi wani aiki ba, a lokacin da nake majalisar dattawa.”

Kano: Kotun Zabe Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Nasarar Abba Gida-Gida

A wani rahoton kuma Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta sanar da ranar yanke hukunci kan nasarar Abba Gida-Gida.

Tawagar lauyoyin NNPP mai kayan marmari ta tabbatar da cewa kotu ta sanya ranar Laraba a matsayin ranar yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262