Ganduje, Gwamnonin APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Dira Jihar Imo

Ganduje, Gwamnonin APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Dira Jihar Imo

  • Dakta Ganduje, gwamnoni, ministoci da wasu ƙusoshin siyasa sun mamaye jihar Imo domin kaddamar da kwamitin kamfe
  • Wannan na zuwa ne a shirye-shirye tunkarar zaben gwamnan jihar wanda zai gudana ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023
  • Shugaban APC zai kaddamar da tawagar yaƙin neman zaben Uzodinma a karo na biyu gobe Asabar 16 ga watan Satumba, 2023

Jihar Imo - Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, wasu gwamnoni da mataimakin kakakin majalisar wakilai, sun dira Owerri, babban birnin jihar Imo.

Manyan ƙusoshin jam'iyyar APC na ƙasa sun mamaye Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya ranar Jumu'a domin kaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamna.

Shugaban APC da tawagarsa zasu je Imo.
Ganduje, Gwamnonin APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Dira Jihar Imo Hoto: thenationonline
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne yayin da ake tunkarar zaben gwamna a jihar Imo ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaoto.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta kafa Kwamitin Mutum 15 Domin Shirya Bukukuwan Samun 'Yancin Kai

Ɗan takarar APC kuma gwamna mai ci, Hope Uzodinma, na neman ta zarce zango na biyu a babban zaɓen jihar mai zuwa nan da wasu 'yan watanni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta sanya ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, 2023 domin gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohin Imo, Kogi da kuma Bayelsa.

Kwamitin kamfen jihar Imo mai ƙunshe da mambobi 69 zai yi aiki ne ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Kuros Riba, Sanata Bassey Otu, rahoton Vanguard.

Wasu daga cikin mambobin kwamitin kamfen APC a Imo

Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru; mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ƙaramin ministan kwadugo, Uche Nnaji da Nkeiruka Onyejeocha su ne jagororin kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin kamfen sun ƙunshi mambobin kwamitin gudanarwa (NWC), gwamnan Ekiti, Abiodun Oyebanji, tsoffin gwamnonin Abia da Imo, Rochas Okorocha da Orji Kalu, da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Ƙara Kassara Jam'iyyar PDP, Jiga-Jigan Mambobi Sun Koma Jam'iyyar APC a Jiha 1

Ayyukan da Ganduje zai yi a jihar Imo

A wata sanarwa da sakataren tsare-tsaren APC, Alhajj Sulaiman Muhammad Arugungu, ya fitar ta nuna cewa shugaban jam'iyya na ƙasa zai kaddamar da kwamitin kamfen a Owerri.

Bayan kaddamar da kwamitin kamfen da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Asabar 16 ga watan Satumba, akwai liyafar za aka shirya wa Ganduje, mambobin NWC da na kwamitin kamfe.

Za a kammala bukukuwan kaddamar da tawagar yakin nenan zaben da taron addu'o'i a Cocin gidan gwamnatin Imo da ke birnin Owerri ranar Lahadi.

Gwamnan APC Ya Tsige Wasu Hadimansa, Ya Naɗa Su a Sabbin Muƙamai

A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sauya wa wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwansa ma'aikatar da zasu yi aiki.

Gwamnan ya sanar da sunayen waɗanda ya canza wa mukamin ne a ranar Juma’a a wurin taron aka saba shirya musu tare da manyan sakatarori na 2023.

Kara karanta wannan

Nasarar APC Ta Fara Tangal-Tangal, Kotun Zaɓe Ta Tanadi Hukunci Kan Zaben Gwamnan Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel