Ganduje Ya Kaddamar Kwamitin Yakin Neman Zabe A Imo, Ya Sha Alwashin Lashe Zabe

Ganduje Ya Kaddamar Kwamitin Yakin Neman Zabe A Imo, Ya Sha Alwashin Lashe Zabe

  • Yayin da zaben gwamna a jihar Imo ke kara karatowa, jam'iyyar APC mai mulki ta kafa kwamitin yakin neman zabe
  • Shugaban jam'iyyar a Najeriya, Dakta Abdullahi Ganduje shi ya kaddamar da kwamitin a yau Asabar 16 ga watan Satumba a jihar Imo
  • Wannan na zuwa ne yayin da hukumar zabe ta saka ranar 11 ga watan Nuwamban 2023 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta kaddamar da kwamitin kamfe na zaben gwamnoni da za a yi a jihar Imo a watan Nuwamba.

Shugaban jam'iyyar, Abdullahi Umar Ganduje shi ya bayyana haka a yau Asabar 16 ga watan Satumba a birnin Owerri na jihar Imo.

Ganduje ya kafa kwamitin zabe a Imo, ya ce APC za ta lashe zabe
Ganduje Ya Sha Alwashin APC Za Ta Lashe Zabe A Jihar Imo. Hoto: APC Nigeria.
Asali: Facebook

Meye Ganduje ya ce kan APC a Imo?

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Imo: Ganduje Ya Bayyana Abun Da Za Su Yi Don Yin Nasara

Ganduje ya ce jam'iyyar su ta shirya tsaf don ganin ta sake lashe zaben gwamnan jihar, gidan talabijin na Channels ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hope Uzodinma shi ne gwamnan jihar da ke neman zarcewa a karo na biyu.

Uzodinma ya yi alkawarin cewa idan ya samu nasara a karo na biyu zai inganta rayuwar al'umma fiye da wa'adinsa na farko.

Wane alwashi Ganduje ya yi kan APC a Imo?

Ganduje wanda shi ya kaddamar kwamitin ya ce jam'iyyar ta na da duk abin da ya kamata na lashen zaben gwamnan a jihar, Voice of Nigeria ta tattaro.

Ya yi alkawarin cewa da jam'iyyar da kuma gwamnatin Bola Tinubu za su bai wa Uzodinma duk wani goyon baya da ya ke bukata.

Yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben, APC ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara kamfen a kananan hukumomi 27 a jihar.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ganduje, Gwamnonin APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Dira Wata Jiha, Bayanai Sun Fito

Ganduje Ya Bayyana Abun Da Za Su Yi Don Yin Nasara a Imo

A wani labarin, Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya yi kira ga mambobin jam'iyyar a Imo da su yi aiki dare da rana don lashe zaben gwamnan jihar da ke tafe a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Ganduje ya roki mambobin jam'iyyar ne yayin da yake kaddamar da hedkwatar kamfen din APC da ke hanyar Wethedral da ke Owerri a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel