Tinubu Ya Yi Magana Daga Kasar Waje Mintuna Bayan Doke PDP da LP a Kotu

Tinubu Ya Yi Magana Daga Kasar Waje Mintuna Bayan Doke PDP da LP a Kotu

  • Atiku Abubakar da Peter Obi ba su iya yin nasara wajen rusa galabar Bola Tinubu a zaben 2023 ba
  • Bola Ahmed Tinubu ya yi farin ciki da hukuncin da kotu ta zartar na ba shi nasara a kan PDP da LP
  • Mai girma shugaban kasa ya yi kira da abokan hamayyarsa su taimaka su marawa gwamnati baya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja – Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi maraba da hukuncin da kotun sauraron karar zaben shugaban kasa ta zartar a yammacin Laraba.

Shugaban Najeriyan ya fitar da jawabi ta bakin Hadiminsa, Ajuri Ngelale, ya na murna da nasarar da ya yi a kan abokan adawarsa a kotun zabe.

Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa mutane cewa zai maida hankali wajen cika alkawuran da ya dauka na kawo zaman lafiya da cigaba a kasa.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Yi Farin Ciki, Ya Yi Magana a Kan Nasarar Tinubu a Kotun Zaben 2023

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya lashe zaben 2023 Hoto: radionigeria.gov.ng
Asali: UGC

Bola Tinubu ya yabi Alkalan kotun zabe

Hukuncin ya kara tabbatar da jajircewa da shirin shugaba Tinubu na hidimtawa daukacin ‘yan Najeriya ba tare da nuna wani bambanci ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabinsa, Cif Ajuri Ngelale ya ce mai gidansa ya jinjinawa Mai shari’a Haruna Tsammani da sauran Alkalai kan yadda su ka fassara doka.

Shugaban kasar ya ce hukuncin korafin zaben ya nuna yadda tsarin shari’ar Najeriya ya cigaba.

Haka zalika, Tinubu ya na ganin abin da ya faru a zaben shugaban kasa da aka yi a farkon bana ya nunawa duniya rikar da Najeriya tayi a siyasa.

Shugaba Tinubu ya sa aiki a gaba

Tun da kotu ta yanke hukunci, shugaban Najeriyan ya yi kira ga abokan hamayyarsa da su bukaci magoya bayansu su bar siyasa, su nuna kishin kasa.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Yi Garaje, Ya Fadi Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Karar Zaben 2023

Jawabin ya ce babu abin da zai taimakawa rayuwar jama’a kamar goyon bayan gwamnati mai-ci.

Tashar NTA ta rahoto mai taimakawa shugaba Tinubu wajen yada labarai da hulda da jama’a ya na kara mika godiya ga ‘yan Najeriya da su ka zabi APC.

Da yardar Ubangiji Madaukakin Sarki, Ngelale ya ce gwamnatin Tinubu ta tanadi mutane da za su dage dare da rana domin cika alkawuran da aka yi.

Atiku bai gamsu da shari'ar ba

A baya aka ji Atiku Abubakar yana cewa kotu ta gabatar da hukunci amma ba ayi mana adalci ba, ya ce sun yi sa’a, tsarin mulki ya yarda a tafi kotun koli.

A cewar lauyan ba za a ce an kai karshe ba sai an tike shari’ar a babban kotun koli na kasa. Chris Uche SAN ya ce hukuncin da aka yi bai yi masu dadi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel