Lauyan Atiku Ya Fara Nuna Matakin da Za a Dauka Bayan Nasarar APC a Kotu

Lauyan Atiku Ya Fara Nuna Matakin da Za a Dauka Bayan Nasarar APC a Kotu

  • Atiku Abubakar wanda ya yi wa jam’iyyar PDP a 2023 bai hakura da shari’ar zaben Najeriya ba
  • ‘Dan takaran shugaban kasar ya nuna bai gamsu ba, da alamun zai daukaka kara zuwa kotun koli
  • Chris Uche, SAN ya shaida cewa su na sa ran samun nasara a kotun gaba, ya nuna ba za su sallama ba

ABUJA – Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ‘dan takaran shugaban kasa a PDP a 2023, Atiku Abubakar bai ji dadin hukuncin kotun zabe ba.

‘Dan takaran ya yi magana ne ta bakin lauyansa Cif Chris Uche, SAN, Vanguard ta kawo rahoton jim kadan bayan kotu ta sanar da hukuncinta a Abuja.

Alhaji Atiku Abubakar ya nuna zai tafi kotun koli domin ya na ganin kotun daukaka kara da ta saurari shari’ar zaben 2023 a jiya ba tayi masa adalci ba.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Yi Farin Ciki, Ya Yi Magana a Kan Nasarar Tinubu a Kotun Zaben 2023

Atiku Abubakar
'Dan takaran PDP a 2023 Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jawabin Lauyan Atiku Abubakar

"An gabatar da hukunci amma ba ayi mana adalci ba. Sai dai mun yi sa’a, tsarin mulki ya ba mu damar daukaka kara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan ne kotun farko. Mu na da damar zuwa kotun koli, kuma wannan gwagwarmaya ba ta wanda mu ke karewa ba ne kurum, na tsarin mulkin kasarmu, dokar kasa da damukaradiyya ne.
Mun yi tsammanin samun hukunci dai zai inganta, ya bada kwarin gwiwar amfani da fasaha domin kula da zabe, a kara gaskiya, kuma a tabbatar da adalci, ta yadda ‘yan Najeriya za su yarda da damukaradiyya."

- Chris Uche SAN

Chris Uche yake cewa ba za su so hukuncin da zai karya gwarin gwiwar mutanen da ke zabe.

Atiku ya na ganin hasken nasara a kotun koli

Lauyan ya ce akwai abubuwan da su ke da ta-cewa a game da su a hukuncin da aka zartar a kotun daukaka kara, ya ce ba su cire tsammanin adalci ba.

Kara karanta wannan

Muhimman Dalilai 5 Da Zasu Iya Sa Kotun Zabe Ta Tsige Shugaba Tinubu Daga Kujerar Mulkin Najeriya

"Mun yi imani kwarai cewa idan mu ka je kotun koli, za a samu damar duba wasu daga cikin abubuwan da aka fada a nan yau.
Mu na da umarni daga wanda mu ka shigarwa kara da mu tafi kotun koli. Saboda haka, mun bukaci bayanai.
Mun bukaci takardar shari’ar. Za mu nemi a aiko mana da takardu domin ba su da lokacin da isasshen lokaci."

- Chris Uche SAN

Abin da Muhammadu Buhari ya fada

Ku na da labari tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce idan har akwai wanda ya yi nasara a yau, to damukaradiyya da kuma al’umma ne.

A wani jawabi da aka samu daga Garba Shehu, Buhari ya ce daga nan, sai sabuwar gwamnatin APC ta nemi goyon baya domin cika alkawuran da tayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel