2023: Buhari Ya Yi Farin Ciki, Ya Yi Magana a Kan Nasarar Tinubu a Kotun Zabe

2023: Buhari Ya Yi Farin Ciki, Ya Yi Magana a Kan Nasarar Tinubu a Kotun Zabe

  • Muhammadu Buhari ya yi jawabi na musamman bayan jin sakamakon hukuncin kotun zaben 2023
  • Tsohon shugaban na Najeriya ya yi maraba da galabar Bola Tinubu a kan abokan hamayyarsa
  • Buhari ya ce damukaradiyya da mutanen kasar nan su ka yi nasara, ya yi kira sabon shugaban kasa

Katsina - Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tofa albarkacin bakinsa a game da hukuncin kotun sauraron karar zaben 2023.

A wani jawabi da ya fitar ta bakin kakakinsa, Garba Shehu, ya ce galabar Bola Tinubu da Kashim Shettima nasara ce ga daukakin ‘yan kasar nan.

Muhammadu Buhari ya yi magana jim kadan bayan kotu ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban Najeriya da aka yi.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari ya taya Bola Tinubu murna Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari: 'Kotun zabe ta kafa tarihi'

Garba Shehu a jawabin yake cewa kotun na PEPC ta yi watsi da korafe-korafe da ra’ayoyi iri-iri, ta kafa tarihi wajen zartar da hukuncin adalci.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi Da Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ganduje, Keyamo, Bala Mohammed Da Sauransu Ke Likimo a Kotun Zaben Shugaban Kasa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tribune ta rahoto Buhari ya na mai cewa lokaci ya yi da APC za ta jinginar da siyasa a gefe guda, sai ta maida hankali wajen shugabanci nagari.

Jawabin Garba Shehu

"Idan har akwai wanda ya yi naasara a yau (Laraba) damukaradiyyarmu da kuma al’umma ne.
Daga nan, sai sabuwar gwamnatin APC a karkashin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta nemi goyon baya domin cika alkawuran da tayi wa mutane."

- Garba Shehu

Fatan alherin Shugaba Buhari

Buhari wanda ya yi mulki tsakanin 2015 da 2023 ya jinjinawa mutanen kasar da su ka zauna lafiya a duk tsawon lokacin yakin zabe har zuwa yanzu.

Baya ga haka, Daily Trust ta ce tsohon shugaban kasar ya yi addu’an cigaba da samun zaman lafiya karkashin gwamnatin magajinsa a Aso Rock.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Zaben da Ɗan Takarar NNPP Ya Samu Nasara a Jihar Kano

A karshe ya taya Mai girma Bola Tinubu da mataimakinsa da jam’iyyar APC murnar samun nasara, ya yi masu addu’ar sauke nauyin da ke wuyansu.

Nasara ta na ga Tinubu

Tun a baya aka ji labari jagora a APC mai-ci, Tolu Bankole ya bugi kirji ya na cewa Atiku Abubakar ko Peter Obi ba za su yi nasara shari’ar zabe ba.

'Dan siyasar ya ce babu wanda ya isa ya yi wa Alkalai barazana duk da an taso kotun karar zabe a gaba domin a ruguza takarar Bola Tinubu a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel