Manyan 'Yan PDP 9 da Suka Gagara Shiga APC, Kuma Suka Cin Dunduniyar Jam'iyyarsu

Manyan 'Yan PDP 9 da Suka Gagara Shiga APC, Kuma Suka Cin Dunduniyar Jam'iyyarsu

  • Rahoton nan ya tattaro kusoshin jam’iyyar PDP da suka ki bayyana goyon bayansu ‘yan takararsu
  • Sanannen abu ne cewa Nyesom Wike da ‘Yan G5 ba su goyi bayan Atiku Abubakar a zaben 2023 ba
  • Chimoroke Nnamani ya tallata Bola Tinubu, Bode George ya ce a zabi Rhodes-Vivour da Peter Obi

1. Nyesom Wike

A makon nan aka ji dalilan da suka jawo Nyesom Wike bai tare da Atiku Abubakar. Gwamnan bai goyon bayan 'Dan Arewa ya cigaba da zama Shugaban kasa.

Shugaban PDP a Ribas, Ambasada Desmond Akawo yana ganin dole shugabanci ya koma Kudu saboda adalci tun da dai Muhammadu Buhari ya yi wa’adi biyu.

2. Bode George

Bode George da ya taba zama mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa yana cikin wadanda ke goyon bayan ‘dan takaran LP a Legas, Gbadebo Rhodes-Vivour

Kara karanta wannan

Makonni 3 Bayan zabe, Shugaban PDP Ya Jero Dalilan Wike na Goyon Bayan Tinubu

A zaben Shugaban kasa da na Gwamna da za ayi a jihar Legas, Cif George bai tare da jam’iyyarsa ta PDP, sai aka ji yana kira Legasawa da su zabi Jam’iyyar LP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

3. Yakubu Dogara

Yakubu Dogara wanda ya dade yana wakiltar Dass/Tafawa Balewa/Bogoro har ya zama Shugaban Majalisar wakilan tarayya yana jan jiki daga wasu ‘Yan takaran PDP.

A lokacin da yake APC, Dogara bai goyi bayan Bola Tinubu ba, da ya koma PDP, yana cikin masu yakar Gwamna Bala Mohammed, ya ce yanzu ‘dan takara yake dubawa.

Nyesom Wike
Nyesom Wike da 'Yan APC Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

4. Ayo Fayose

Wani jagora a PDP da aka rasa gane kan shi a 2023, shi ne Ayo Fayose wanda ya yi Gwamna a Ekiti, yana cikin wadanda suka raba daya biyu a jam’iyyar adawar.

Kwanaki an yi tunanin tsohon gwamnan Ekitin ya bar PDP, daga baya ya fito ya tabbatar da bai sauya-sheka ba, amma ya ce ya matsa gefe kuma ya bar takara.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Tsorata Kafin Ranar Zabe, Ya Kai Karar ‘Dan Takaran APC Wajen Buhari

5. Chimoroke Nnamani

Wani fitaccen ‘Dan jam’iyyar PDP da ya fito karara ya rika tallata Bola Tinubu shi ne Chimoroke Nnamani wanda yake wakiltar Enugu ta gabas a majalisar dattawa.

A karshe PDP ta kori tsohon Gwamnan kuma ta sanar da Hukumar INEC cewa ta janye takararsa. Nnamani bai sauya-sheka ba duk da ya ki bin Atiku Abubakar.

Sauran wadanda suka juyawa ‘yan takaran PDP baya:

6. Okezie Ikpeazu

7. Ifeanyi Ugwuanyi

8. Samuel Ortom

9. Seyi Makinde

Siyasar Kano sai Kano

Idan aka tsallaka Kano, rahoto ya zo cewa Jam’iyyar NNPP ta shiga dangi, ta tsamo kanin mahaifiyar ‘dan takarar Gwamnan APC, Nasiru Yusuf Gawuna.

Bayan haka Nasir Auduwa Gabasawa mai wakiltar Gezawa/Gabasawa a majalisar tarayya ya koma NNPP yayin da ake saura 'yan kwanaki a shiga zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel