Yayan Uwar Gawuna, 'Dan Majalisar APC, ‘Yan ADP, Sun Shiga Jam’iyyar NNPP a Kano

Yayan Uwar Gawuna, 'Dan Majalisar APC, ‘Yan ADP, Sun Shiga Jam’iyyar NNPP a Kano

  • NNPP ta karbi baffan ‘dan takarar Gwamnan APC, Shehu Tijjani Hassan Gawuna a jihar Kano
  • Hon. Nasir Auduwa Gabasawa wanda yake majalisa a karkashin APC mai-rinjaye ya sauya-sheka
  • Kyaftin Mansur Kurugu da Kwamred Akibu Hamisu duk sun shigo Jam’iyyar NNPP daga ADP

Kano - Siyasar jihar Kano ta na cigaba da daukar wani irin fasali musamman a ‘yan kwanakin nan da jam’iyyar adawa ta NNPP ta ke ta samun karuwa.

Wasu ‘yan siyasa da wadanda ake ganin su na da ta-cewa a zaben sabon Gwamna da za a shirya a jihar Kano, su na tsalle zuwa jam’iyya mai kayan dadi.

Salisu Yahaya Hotoro wanda Darektan yada labarai da sadarwa ne a kwamitin yakin zaben NNPP ya bada sanarwar kabar Shehu Tijjani Hassan Gawuna.

Hotoro ya fitar da wani gajeren jawabi a dandalin Facebook dazu yana cewa Sheikh Shehu Tijjani Hassan Gawuna ya bar jam’iyyar APC, ya shigo NNPP.

Wanene Sheikh Shehu Tijjani Hassan Gawuna?

Sheikh Shehu Tijjani Hassan Gawuna ‘danuwan mahafiyar Nasiru Yusuf Gawuna ne wanda shi ne yake yi wa jam’iyyar APC takarar Gwamna a Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda bayanin da hotuna suka nuna, Shehu Tijjani Hassan Gawuna ya yi zama da jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso bayan a yau.

Kanin Uwar Gawuna
Shehu Tijjani Hassan Gawuna a NNPP Hoto: @salisuyahayahototo
Asali: Facebook
"Sheikh Shehu Tijjani Hassan Gawuna wan mahaifiyar dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin tutar jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya ajiye tafiyar APC ya dawo jam’iyyar NNPP a wannan rana inda Jagora Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karbe shi."

- Salisu Yahaya Hotoro

Wani daga cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben NNPP a matakin shugaban kasa, Ibrahim Adam ya tabbatar da wannan labari a shafinsa a yau Alhamis.

Malam Ibrahim Adam ya kira wannan shirin zabe da NNPP take yi da Operation tsaman dangi.

NNPP ta samu 'Dan majalisa

Saifullahi Hassan, Hadimin Rabiu Kwankwaso da ya nemi takarar shugaban kasa a NNPP ya kuma tabbatar da cewa Hon. Nasir Auduwa Gabasawa ya bar APC.

Auduwa Gabasawa shi ne mai wakiltar Gezawa/Gabasawa a majalisar tarayya a karkashin APC.

ADP ta rasa 'Ya 'yanta

A wani rahoton dabam, Legit.ng Hausa ta ji Darektan labarai da dabaru a kwamitin takarar Sha’aban Shararada, Mansur Kurugu ya sauya-sheka jiya.

Mansur Kurugu da Kwamred Akibu Hamisu wanda shi ne Sakataren kungiyar Fitilar Jama’ar Kano sun bar ADP, sun karbi tafiyar Abba Gida Gida a 2023.

"Za mu ci zabe" - Abba Gida Gida

Legit.ng Hausa ta zanta da Salisu Hotoro wanda ya tabbatar mana da cewa su na hangen nasarar Abba Yusuf a zaben ranar Asabar, ya ce su na sa ran cin zabe.

Hotoro ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta na cigaba da samun karbuwa a yankunan Kano ta Arewa, ya ce ayi watsi da rade-radin cewa ba za a zabe su ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel