Makonni 3 Bayan Zabe, Shugaban PDP Ya Jero Dalilan Wike na Goyon Bayan Tinubu

Makonni 3 Bayan Zabe, Shugaban PDP Ya Jero Dalilan Wike na Goyon Bayan Tinubu

  • Desmond Akawo ya ce saboda mulki ya bar Arewa ne jihar Ribas ta zabi Asiwaju Bola Tinubu
  • Shugaban PDP na Ribas ya nuna babu adalci idan shugaban kasa bai fito daga Kudu a 2023 ba
  • Ambasada Akawo ya ce bayan shekaru 8 ana fada da gwamnatin tarayya, jihar ta hade da sama

Rivers - Shugaban jam’iyyar PDP na reshen jihar Ribas, Desmond Akawo, ya yi magana a kan goyon bayan da Asiwaju Bola Tinubu ya samu.

Daily Trust ta ce bayanai sun fito daga shugaban jam’iyyar kusan makonni uku bayan an yi zabe inda APC tayi galaba a kan jam’iyyun PDP da LP.

Ambasada Desmond Akawo ya bayyana hikimar da ta sa Gwamna Nyesom Wike ya goyi bayan Asiwaju Bola Tinubu, har ya yi nasara a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Ya Yi Kira da Babbar Murya, Ya Fadawa Tinubu Bukatar Yarbawa a Mulkinsa

Desmond Akawo ya yi maganar a garin Fatakwal yayin da yake tattaunawa da wasu kungiyoyi na magoya bayan APC da masoya Asiwaju Tinubu.

An fito da Shugaban kasa daga Kudu

An rahoto Ambasada Akawo yana cewa jam’iyyarsu ta marawa APC baya a zaben shugaban kasa ne saboda tana so mulkin Najeriya ya koma Kudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wike.
Sanwo Olu, Shettima, Tinubu, Wike da Adamu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC
Dalilinmu na goyon bayan Asiwaju shi ne mulki ya koma Kudu. Ko dai Asiwaju ko Obi, dole sabon shugaban kasa ya fito daga Kudu saboda ayi adalci.
Sannan kuma jihar Ribas ta sake hadewa da gwamnatin tarayya. A shekaru takwas da suka wuce, fada aka rika yi, Ribas tana ta rikici da gwamnati.
Yanzu sai muka ce wannan rigima ba za ta cigaba ba. Mu a jihar Ribas (Gwamna Nyesom Wike) ya hada mu da asalin tulun gwamnati a kasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Zama da Zababbun Sanatoci da ‘Yan Majalisa, Ya Yi Maganar ‘Dan Takaransa

- Nyesom Wike

A game da zaben Gwamna

A siyasar gida, Akawo ya ce ganin duk Gwamnonin da aka yi daga 1999 sun fito daga Gabas Ko Yammacin Ribas ne, a bana an tsaida mutumin Ribas ta Kudu.

Ambasada Akawo yake cewa Sim Fubara zai zama ‘dan autan Gwamnonin Najeriya.

Jagoran jam’iyyar APC a jihar Kudu maso kudun, Tony Okocha ya shaidawa shugaban na PDP cewa yadda Wike ya goyi bayansu, za su zabi Fubara.

Omisore v Lukman

Mataimakin Shugaban APC ya ce Sakataren jam’iyya na kasa ya lakume kudin yin kamfe a jiharsa, an samu rahoto cewa wannan magana ta jawo za a je kotu.

Sanata Iyiola Omisore yana neman diyyar N500m saboda zargin bata masa suna.Lauya ya rubuta takarda, yana neman Lukman ya janye kalamansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel