Zaben Jihohi: Gwamnoni da ‘Yan Takara 11 da Ke Cikin Dar-Dar Bayan Zaben Shugaban Kasa

Zaben Jihohi: Gwamnoni da ‘Yan Takara 11 da Ke Cikin Dar-Dar Bayan Zaben Shugaban Kasa

  • A mako mai zuwa za a shirya zaben Gwamnonin jihohi a jihohi fiye da 20 da ke kasar nan
  • Hakan na zuwa ne bayan an gudanar da zaben sabon shugaban kasa a makon da ya wuce
  • Har yanzu akwai sauran aiki a gaban jam’iyyun APC da kuma PDP a wasu jihohin Najeriya

Wannan rahoto ya tattaro jihohin da ake ganin zaben Gwamnonin zai yi zafi a makon gobe.

Jihohin nan da ake tunanin APC, PDP da LP ko NNPP za su gwabza sun hada da Benuwai, Abia, Enugu, Delta, Kano, Kaduna, Filato, Katsina da Gombe.

1. Legas

Ganin yadda jam’iyyar LP ta kunyata Bola Tinubu, dole hankalin Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya tashi. Akwai yiwuwar LP da PDP su hada-kai domin su doke APC.

Manya su na kara nuna goyon baya ga Gwamna, amma yana fuskantar kalubale daga yankin da bare ke zama - wadanda su ka sha alwashin kifar da gwamnati mai-ci.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta Kunshe Biliyoyin Kudi Wajen Saida Fam Ga Masu Sha’awar Takara

2. Oyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin PDP uku da ke cikin G5 sun rasa takarar Sanata da suka nema, a cikin Seyi Makinde ne kurum yake neman tazarce, kuma da alamun sai ya yi da gaske.

Gwamnan na Oyo ya taimakawa wajen shan kashin Atiku Abubakar a makon jiya, babu mamaki magoya bayan Atiku a jihar su yi masa zagon-kasa, su zabi APC.

3. Enugu

Wata jiha da LP tayi amfani da damar rikicin PDP ita ce Enugu, a zaben Gwamna akwai yiwuwar Ifeanyi Ugwuanyi ya sake shan kunya, a doke ‘dan takaransa na PDP.

Punch ta ce Peter Mbah da yake neman Gwamna a PDP zai kara da Uchenna Nnaji, Frank Nweje Jnr da Chijioke Edeoga na jam’iyyun adawar APC, APGA da LP.

4. Abia

Rahoton ya ce Okezie Ikpeazu ya kai kasa a zaben majalisar dattawa a hannun Enyinnaya Abaribe kamar yadda jam’iyyar LP tayi galaba a jihar a makon jiya.

Kara karanta wannan

Saura Watanni 2 Ya Bar Ofis, Buhari Ya Karfafi Muhimmin Aikin da Ya Tattago a Arewa

Ganin nasarorin APC da LP a jihar Abia, babu tabbacin Okey Ahiwe zai gaji uban gidansa a siyasa musamman da zai fuskanci Ikechi Emenike da Dr Alex Otti.

5. Benuwai

Wata Jihar da ta shiga gungun G5 ita ce Benuwai da Gwamnanta da ya goyi bayan Peter Obi ya gagara lashe zaben Sanatan Benuwai ta Arewa maso yamma.

A zaben da ya wuce, APC ta lashe kujerun majalisar tarayya 10, aka bar PDP da daya. Sai PDP tayi da gaske za ta doke Rabaren Hyacinth Alia da Herman Hembe.

Zaben Jihohi
El-Rufai, Lalong, Bello da Ganduje a taro Hoto: BBCnewsHausa
Asali: UGC

6. Delta

Sakamakon zaben shugaban kasa ya nuna babu tabbacin PDP za ta cigaba da mulki a Delta, Gwamna Ifeanyi Okowa bai iya kawowa Atiku Abubakar nasara ba.

Ganin APC ta samu Sanatoci biyu ya nuna akwai aiki a gaban Sheriff Oborevwori mai sa ran doke Ovie Omo-Agege na APC, Great Ogboru na APGA da 'Yan LP.

7. Kuros Ribas

Kara karanta wannan

Shekarau da Jiga-Jigan 'Yan siyasa 8 da Suka Tafka Asara 10 da 20 a Zaben Bana

Farfesa Ben Ayade bai iya doke Agom Jarigbe a zaben zama Sanata ba, abin da hakan ya nuna shi ne PDP da LP za su kalubalanci ‘dan takaran APC, Bassey Otu.

Duk da karfin Farfesa Sandy Onor da Ernest Obasse masu neman Gwamna a PDP da LP, jam’iyyar APC ta lashe fiye da rabin kujerun majalisar wakilan jihar.

8. Filato

Mutane uku ne kan gaba wajen neman gwamnan jihar Filato a zaben 2023; Dr. Nentawe Yilwatda, Caleb Mutfwang da Dr Patrick Dakum a PDP, APC da LP.

A zaben shugaban kasa da aka yi, LP tayi nasara sannan jam’iyyar PDP ta lashe kujeru hudu na majalisar wakilai da dattawa, wannan ya kada hantar APC.

9. Kaduna

A Kaduna, Nasir El-Rufai bai ji dadin sakamakon zaben shugaban kasa ba, wannan ya sa dole sai ‘dan takaransa watau Uba Sani ya dage zai iya lashe zaben jihar.

PDP za ta sa ran maimaita abin da ya faru a makon jiya domin Isa Ashiru Kudan ya zama Gwamna, watakila hakan ya jawo Jam’iyyar ta hada-kai da LP a Kudu.

Kara karanta wannan

Lauje cikin nadi: Dan takarar gwamnan NNPP a Arewa ya ce bai amince da sakamakon zabe ba, zai tafi kotu

10. Kano

A Kano sai Nasir Yusuf Gawuna ya dage zai iya kai labari musamman idan aka lura da yadda guguuwar Rabiu Kwankwaso tayi wa APC barna a NNPP.

Akwai yiwuwar sauran ‘yan jam’iyyun hamayya su hada-kai da Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC domin a iya takawa Abba Kabir Yusuf burki a 2023.

11. Katsina

Tuni Gwamna Amini Bello Masari yake ta korar ‘ya ‘yan APC da ake zargin sun bada gudumuwa wajen nasarar da PDP ta samu a mahaifar shuagaban kasa.

Muddin ba a dauki mataki ba, Sanata Yakubu Lado Danmarke na jam’iyyar adawa ta PDP yana iya hana Dr. Umar Dikko Radda zama magajin Masari a APC.

An yi canji a Majalisa

Ku na da labari Majalisar Dattawa tayi ban-kwana da Ike Ekweramadu (PDP), Kabiru Gaya (APC) da James Manager (PDP) bayan tsawon shekara da shekaru.

Sannan ‘Yan majalisar wakilan da za a rasa a 2023 sun kunshi: Leo Ogor, Yakubu Dogara da Ndudi Elumelu da suka dade su na lashe zaben mazabunsu.

Kara karanta wannan

Duk da Guguwar Peter Obi, Jam’iyyar LP Ta Gaza Samun Gwamna ko 1 a Zaben Jihohi

Asali: Legit.ng

Online view pixel