Shekarau da Jiga-Jigan 'Yan siyasa 8 da Suka Tafka Asara 10 da 20 a Zaben Bana

Shekarau da Jiga-Jigan 'Yan siyasa 8 da Suka Tafka Asara 10 da 20 a Zaben Bana

  • A 2023 da aka yi, akwai ‘yan siyasan da suka gamu da rashi, akwai wadanda suka yi nasara
  • A cikin wadanda suka yi rashi a bana, akwai wasu da asara biyu ta auka masu a filin zabe
  • Wasu sun shiga takara sun fadi, sannan sun tsaida ‘yan takararsu, a nan ma ba su yi dace ba

Jaridar Daily Trust ta jero ‘yan siyasar da ake gani sun yi asara biyu a zaben nan, sun hada:

1. Yakubu Dogara

Rt. Hon. Yakubu Dogara ya fita daga APC, ya marawa Atiku Abubakar baya a zaben shugaban kasa a karshe kuma jam’iyyar da ya bari ta doke ‘dan takaransa.

A zaben Gwamnan Bauchi, Yakubu Dogara ya rabu da Gwamna Bala Mohammed na jam’iyyarsa, ya goyi bayan APC, a nan ma ya burma masu da kafar hagu.

Kara karanta wannan

Atiku: Yadda Aka Yi Amfani da Wata Na’ura, Aka Zaftare Mani Kuri’u a Zaben 2023

2. Okezie Ikpeazu

Okezie Ikpeazu ya yi yunkurin zama Sanata a 2023, amma jam’iyyar LP ta tika shi da kasa. Bayan makonni LP ta sake doke ‘dan takarasa a zaben Gwamnan Abia.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai girma Okezie Ikpeazu ya na cikin ‘Yan G5 da suka yi fada da Atiku Abubakar a jam’iyyar PDP.

3. Samuel Ortom

A zaben wannan karo, Gwamna Samuel Ortom ya tashi babu tsuntsu babu tarko domin Peter Obi da yake tare da shi bai yi nasara a zaben sabon shugaban kasa ba.

Haka zalika Mai girma Samuel Ortom ya kunyata a zaben Sanatan Arewa maso Yammacin Benuwai, a karshe APC ta doke wanda PDP ta tsaida takara a jiha.

4. Ifeanyi Ugwuanyi

Ifeanyi Ugwuanyi yana tare da Gwamnonin Abia da Benuwai a nan, Okechukwu Ezea na LP ya doke shi a zaben Sanata, amma a karshe Peter Mba zai gaji kujerarsa.

Kara karanta wannan

Ana Neman Hana Tinubu Hawa Mulki, Atiku Ya Kinkimi Lauyoyi, An Garzaya Kotun Zabe

5. Bukola Saraki

Da farko Dr. Bukola Saraki ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a PDP amma bai yi nasara ba, a babban zabe kuma ‘dan takararsa, Atiku Abubakar ya sha kashi.

Tambuwal
Sule, Saraki da Tambuwal Hoto: www.premiumtimesng
Asali: UGC

A zaben Gwamna da majalisu, jam’iyyar APC ta koyawa tsohon Gwamnan da PDP hankali a Kwara. Kusan Saraki bai tashi da komai a 2023 ba, kamar dai a 2019.

6. Sule Lamido

Wani jigo a PDP da zai so ya manta abin da ya faru a zaben nan shi ne Sule Lamido wanda bai iya ba Atiku Abubakar da jam’iyyarsa nasara a zaben shugaban kasa ba.

A zaben Gwamna a jihar Jigawa, tsohon Ministan yana kallo ‘dan takaran jamiyyar APC ya doke Mustafa Sule Lamido, sannan PDP ba ta samu kujerun majalisa ba.

7. Aminu Tambuwal

Aminu Tambuwal ya taimakawa Atiku Abubakar wajen samun tikitin PDP, amma babu yadda ya iya yayin da Bola Tinubu ya zama zababben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Duk da Guguwar Peter Obi, Jam’iyyar LP Ta Gaza Samun Gwamna ko 1 a Zaben Jihohi

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya rasa jihar Sokoto domin Ahmed Aliyu ya doke ‘dan takarsa, Saidu Ubandoma. Sannan batun zamansa Sanata a 2023 ya na lilo

8. Simon Lalong

A matsayinsa na Darektan yakin neman zaben Bola Tinubu, APC ba ta lashe zaben shugaban kasa a jihar Filato ba, duk da Simon Lalong yana kan kujerar Gwamna.

Haka zalika a zaben sabon Gwamna, Jam’iyyar PDP ta doke Dr. Nentawe Yiltwada.

9. Ibrahim Shekarau

Jam'iyyar NNPP ta ba Malam Ibrahim Shekarau tikitin Sanata, amma ya watsar, ya koma PDP. A karshe Atiku Abubakar bai yi nasara ba, NNPP kuma ta ci zabe.

Shugabancin majalisa a 2023

Shekaru takwas da zuwa Majalisar Dattawa, an samu labari Sanatan Barau Ibrahim Jibrin yana harin zama shugaba, shi kadai ne Sanatan APC a jihar Kano.

Watakila takarar wannan karo ta kasance tsakanin Barau Jibrin, Uzor Kalu da David Umahi. Kafin zamansa Sanata, Jibrin ya je Majalisar wakilan tarayya.

Kara karanta wannan

Wasu ‘Yan Takaran APC Za Su Kotu Domin Karbe Nasarar PDP a Zaben Gwamnoni

Asali: Legit.ng

Online view pixel