Saura Watanni 2 Ya Bar Ofis, Buhari Ya Karfafi Muhimmin Aikin da Ya Tattago a Arewa

Saura Watanni 2 Ya Bar Ofis, Buhari Ya Karfafi Muhimmin Aikin da Ya Tattago a Arewa

  • Gwamnatin tarayya ta amince a batar da N453.90bn wajen sayen kayan aikin titin jirgin kasa
  • Kamfanin Kamfanin MSSRs Mota-Engil Nigeria Ltd yana gina hanyar jirgin kasan Kano-Maradi
  • A taron da shugaban kasa ya jagoranta, an amince da takardun da Ma’aikatar sufuri ta kawo

Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi na’am da kashe N453.90bn domin sayen kayan aiki da na gyare-gyaren dogon Kano zuwa Maradi da ake ginawa.

Majalisar zartarwa watau FEC ta amince da wannan mataki a zaman da aka yi na ranar Larabar nan, labarin ya fito ne a jaridar Punch ta kasar nan.

Kudin da aka amince a batar a taron FEC din sun hada da N510.93m na sayen motocin kwana-kwana na kashe wuta a tashoshin Fatakwal da Legas.

Mai girma Ministan sufuri na kasa, Mu’azu Sambo ya tabbatar a wannan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen zaman da aka yi a jiya.

Aikin jirgin Kano - Maradi

A shekarar 2021 aka dauko wannan aikin jirgin kasa na kilomita 284 wanda zai ratsa Kano zuwa Kazaure, Bauchi, Daura, Mashi, Katsina har Jibiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aikin zai karkare ne a garin Maradi da ke Jamhuriyyar Nijar, kasar da ke iyaka da Katsina.

Taron FEC
Taron FEC a Aso Rock Hoto: @Buhari Sallau
Asali: Facebook

A wancan lokacin, Rotimi Amaechi an ce titin zai kunshi tashohi 15, kuma ana ran a rika samun fasinjoji 9364 a rana dauke da metric ton 3000 na kaya.

Jawabin Ministan sufuri

An rahoto Mu’azu Sambo yana cewa sun bijiro da batun wannan kwangila a gaban Ministocin tarayya domin amincewa a sayo wasu kayayyakin aiki.

Ma’aikatar sufurin ta nemi amincewar FEC domin a saye kayan gyaran dogon, kuma an amince. Kamfanin MSSRs Mota-Engil Nigeria Ltd suke aikin.

Ministan ya ce sun gabatar da takarda a madadin NPA domin kamfanin All Works Commercial Company Limited ya samar da motocin kashe gobara.

Ministan gona na kasa, Mohammed Abubakar, ya yi wa manema labarai magana yana cewa FEC ta yi na’am da takardun da suka gabatar a zaman.

Shari'ar Atiku Abubakar v PDP

A rahoton da mu ka fitar a baya, an ji Lauyoyin Atiku Abubakar sun sha alwashin sai sun karbe nasarar da Bola Tinubu ya samu a zaben 2023

Babban Lauyan ‘Dan takaran, Joe-Kyari Gadzama ya ce INEC sun rika tace sakamako kafin a daura IRev, wanda hakan ya jawo APC tayi magudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel