Yadda Aka So Ayi Amfani da Tinubu Wajen Cin Amanar Buhari a 2019 – Gwamnan PDP

Yadda Aka So Ayi Amfani da Tinubu Wajen Cin Amanar Buhari a 2019 – Gwamnan PDP

  • Nyesom Wike ya bada labarin yadda suka lallabi Bola Tinubu ya yi wa PDP aiki a zaben 2019
  • Gwamnan jihar Ribas yake cewa Tinubu ya ki yarda ya goyi bayan ‘yan takaran jam’iyyar PDP
  • A karshe ‘Dan siyasar ya ce Muhammadu Buhari zai marawa baya a maimakon su Atiku Abubakar

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce Asiwaju Bola Tinubu ya rikewa Shugaba Muhammadu Buhari amana a lokacin zaben 2019.

The Cable ta rahoto Nyesom Wike yana bayanin cewa ya zauna da Bola Tinubu a gidansa, ya roke shi ya goyi bayan Atiku Abubakar ko waninsa.

A wancan lokaci, jagoran na jam’iyyar ya nuna ba zai ci amanar Mai girma Muhammadu Buhari ba, ya gwammace shugaban kasar ya zarce.

Gwamnan na PDP yake cewa shi da kan shi ya je gidan Tinubu domin nemawa Atiku da sauran masu neman takara goyon baya, amma ya ki yarda.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamna Wike Ya Yi Magana Ta Karshe Kan Yuwuwar Sulhu da Atiku Ana Dab da Zaɓen 2023

Tinubu - Buhari
Buhari da Tinubu ana kamfe Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya zauna da Tinubu

Mista Wike ya yi zama da ‘dan takaran na APC a yau ne bayan wasu zama da ya yi da shugaban majalisar dattawa da Gwamnan Sokoto a 2017 da 2018.

"Na zo gidanka Bourdillon na kawo ziyara, na fada maka ‘dubi yadda kasa ta ke tafiya; ba za ta yiwu ka bar shugaban nan ya cigaba a 2019 ba.
Sai ka tambaye ni; ‘Su wanene madadin da ake da su?’ Sai na fada maka cewa mu na Atiku Abubakar, mu na da Tambuwal, mu na Bukola.
Sai kayi dariya, ka fada mani ‘gara in tsaya tare da Buhari, idan wadannan ne ku ke da su, to zan tsaya tare da shugaba Muhammadu Buhari.

- Nyesom Wike

Rahoton ya ce Gwamnan ya yi maganar alaka da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce Bola Tinubu yana da halayen shugaban da ake bukata.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya ne: Tinubu ya fadi abu 1 da zai yiwa ASUU kowa ma ya huta idan ya gaji Buhari

Wike ya soki Gwamnan CBN

The Nation ta ce Gwamna Wike ya soki yadda babban bankin kasa watau CBN ya ki yin biyayya ga umarnin kotun koli a kan amfani da tsofaffin kudi.

"Ya za ku zama ku na da gwamnati a yau, amma Gwamnan babban banki yana bijirewa kotun koli? Ina ake haka a tsarin damukaradiyya?"

- Nyesom Wike

Abin da ake tsoro - Shehu Sani

A wani rahoto, an ji Shehu Sani yana cewa a lokacin da majalisar tarayya ta amince da kudirin da ya zama dokar canza kudi, ba a fahimci tasirin ba.

Tsohon Sanatan yake cewa ba a wayar da kan mutane sosai ba, sai kwatsam yanzu aka fahimci cewa tsarin yana tasiri a kan rayuwar kowa a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel