ASUU Ba Za Ta Tafi Yajin Aiki Ba a Lokacin da Nake Mulki, Inji Dan Takarar Shugaban Kasan APC, Tinubu

ASUU Ba Za Ta Tafi Yajin Aiki Ba a Lokacin da Nake Mulki, Inji Dan Takarar Shugaban Kasan APC, Tinubu

  • Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ya bayyana cewa, ASUU za ta daina yaji idan ya hau mulki
  • Tinubu ya ce PDP ta sace dukiyar kasa, don haka Buhari yazo ya kawo gyara mai yawa, shi kuwa zai daura
  • Gwamnan jihar Imo ya yiwa Tinubu alkawarin cewa, ‘yan jiharsa za su zabi APC a zaben 2023 mai zuwa nan kusa

Jihar Imo - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya fada a ranar Talata cewa, yajin aikin da malaman jami’a na ASUU ke yi zai zama tarihi idan ya zama shugaban kasan Najeriya.

Ya kuma yi alkawarin samar da shiri na ci gaba da ayyukan da shugaban kasa Manjo Muhammadu Buhari mai ritaya ya fara, rahoton Punch.

Ya ce, shekaru takwas na mulkin Buhari shimfidar kayan aiki ne, inda yace zai zuba kudin kasa a fannin ilimi da ababen more rayuwa matukar ‘yan Najeriya suka zabe shi.

Kara karanta wannan

Shin karancin Naira zai shafi zaben bana? Jami'in INEC ya yi gargadi mai daukar hankali

Tinubu ya yiwa alkawari mai girma ga ASUU
ASUU Ba Za Ta Tafi Yajin Aiki Ba a Lokacin da Nake Mulki, Inji Dan Takarar Shugaban Kasan APC, Tinubu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Tinubu ya yi wadannan alkawura ne a filin taron kamfen dinsa da aka gudanar a filin wasanni na Dan Anyiam da ke birnin Owerri a jihar Imo, rahoton Daily Sun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Ba za a sake samun yajin aikin ASUU ba a Najeriya. Za a gama kowane karatu a lokacinsa. Misali, duk wani digirin shekara hudu za a gama shi a karshen shekaru hudu a jami’a.”

PDP ta sace kudin kasa, cewar Tinubu

Da yake caccakar jam’iyyar PDP da yadda ta yi mulki a shekarun baya, Tinubu ya bayyana cewa:

“PDP ta sace arzikin Najeriya. Shekaru takwas na shugaba Buhari gyara ne ga tsarin. PDP makaryata ne. Za mu ci gaba da shirye-shiryen ci gaba na APC, ba zai tsaya ba.”

Mai masaukin baki, gwamna Hope Uzodinma ya ce, jihar Imo ta karbi tafarkin APC kuma tabbas mutanen jihar za su ba Tinubu kuri’usu a zaben bana, ba za su ba shi kunya ba.

Kara karanta wannan

Ba Gwamnan Arewan da Zai Iya Kawowa Tinubu Kuri'un Jiharsa, Tsohon Shugaban NHIS

Dole magajin Buhari ya yi koyi dashi, inji Boss Mustapha

A wani labarin kuma, sakataren gidan gwamnati, Boss Mustapha ya bayyana irin alheran shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Boss ya bayyana cewa, ya kamata duk wani shugaban da ya samu nasarar lashe zaben bana ya yi koyi da Buhari don ci gaban kasa.

Saura kwanaki kadan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka, ana jiran wanda zai gaje shi bayan zaben 25 ga watan Faburairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel