Abin da ya sa Suke Fada da Canjin Kudi – Tsohon Sanatan APC Ya Tona Asirin Gwamnoni

Abin da ya sa Suke Fada da Canjin Kudi – Tsohon Sanatan APC Ya Tona Asirin Gwamnoni

  • Akwai manufar da ta sa Gwamnonin Jihohi ba su goyon bayan canza kudi a ra’ayin Shehu Sani
  • Tsohon 'dan majalisar ya ce tsarin ya gamu da adawa ne saboda an fito da shi kafin zaben 2023
  • Sanata Shehu Sani ya ce Gwamnonin su na neman yadda za su saye kuri’un talakawa wajen zabe

Abuja - Shehu Sani wanda ya yi shekaru hudu a majalisar dattawa, ya yi bayanin abin da ya jawo gwamnonin jihohi ba su goyon bayan canjin kudi.

A wata zantawa da ya yi da tashar talabijin Channels a ranar Laraba, Sanata Shehu Sani ya zargi gwamnonin Najeriya da shirin sayen kuri’un jama’a.

Shehu Sani yake cewa da a ce bayasn zaben 2023 ne za a canza wasu daga cikin takardun kudin kasar, da gwamnonin jihohi za su goyi bayan tsarin.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Bayyana Yadda Buhari da CBN Suka Jawowa Jam’iyyarsu Bakin Jini

An tattauna da ‘dan siyasar ne a shirin “The 2023 Verdict” domin jin ra’ayinsa game da batun.

Zargin da Shehu Sani yake yi

“Hakikanin dalilan da suka jawo Gwamnoni suke adawa da canjin takardun Naira da tsarin takaita yawon kudi shi ne su na so sayen kuri’u da tsofaffin kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da a ce sai bayan zabe za a sauya kudin, da babu wani ‘dan siyasa da zai kalubalanci tsarin ko ya yi adawa.

- Shehu Sani

Gwamnoni
Gwamnoni a Fadar Aso Rock Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Kuskuren da aka yi - Shehu Sani

Premium Times ta rahoto tsohon ‘dan takaran Gwamnan na Kaduna yana cewa gwamnati ba ta tafi da jama’a wajen kawo wadannan sababbin tsari ba.

"A lokacin da majalisar tarayya ta amince da kudirin ya zama doka, ba a tafka muhawara sosai, a tattauna domin a fahimci tasirin canza kudin ba.

Kara karanta wannan

Tattaunawa: Lauya Ya Shawarci INEC Kan Yadda Zasu Dakile Sayen Kuri'u

Ba a wayar da kan mutane sosai ba, saboda haka ba a tafi da su ba, sai kwatsam yanzu aka fahimci cewa tsarin yana tasiri a kan rayuwar kowa."

- Shehu Sani

Sanata Sani ya ce kafin a dauki mataki irin wannan, ya kamata a zauna da jama’a, a wani rahoton kuma, Kwamred ya ce shugaban kasa bai fahimci abin ba.

Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, ya ce Muhammadu Buhari bai da ilmin tattalin arziki, don haka tun farko CBN ya rude shi.

Rotimi Akeredolu ya koka

Gwamnoni irinsu Nasir El-Rufai, Yahaya Bello, Bello Matawalle, Abdullahi Ganduje, Nyesom Wike, Rotimi Akeredolu duk sun soki shirin na bankin CBN.

Rotimi Akeredolu yana ganin cewa tsarin sauya takardun kudi da kudi da CBN ya fito da shi, bai yi komai ba illa karawa jam’iyyar APC bakin jini a zaben bana.

An rahoto Gwamnan Ondo yana cewa a halin yanzu abubuwa sun yi wuya a kasar, don haka tsarin bai zo a lokacin da ya kamata ba, ya nemi a soke shi.

Kara karanta wannan

Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

Asali: Legit.ng

Online view pixel