Gwamna Wike Ya Kore Yuwuwar Sulhu Tsakanin G5 da Atiku Gabanin Zaɓen 2023

Gwamna Wike Ya Kore Yuwuwar Sulhu Tsakanin G5 da Atiku Gabanin Zaɓen 2023

  • Gwamnan jihar Ribas ya ce ba maganar sulhu tsakanin tsagin G5 da shugabancin PDP na ƙasa karkashin Ayu
  • Nyesom Wike, jagoran tawagar gaskiya a PDP ya ce ba wanda zai ƙara zama da shi da nufin sasantawa da Atiku
  • Gwamnan ya faɗi matsayarsa ta karshe ne kwana ɗaya bayan an hangi Tinubu ya kai masa ziyara a Patakwal

Rivers - Kwana 9 gabanin zaɓen shugaban kasa, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya kore duk wata yuwuwar samun sulhu tsakanin G-5 da Atiku Abubakar.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa ba zai ƙara zama da wani ɗan tsagin Atiku ba da nufin neman maslaha tsakanin G-5 da shugabancin PDP na ƙasa karkashin Iyorchia Ayu.

Gwamna Nyesom Wike.
Gwamna Wike Ya Kore Yuwuwar Sulhu Tsakanin G5 da Atiku Gabanin Zaɓen 2023 Hoto: Nyesom Wike.
Asali: UGC

Wike ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da manema labarai ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu, 2023, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Ka Bani Mamaki" Gwamna Wike Ya Maida Martani Ga Jawabin Shugaba Buhari Kan Karancin Naira

Ya ce ba wanda zai ba hakuri don ya karɓi bakuncin ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Ahmed Tinubu, a Patakwal ranar Laraba bayan Ralin kamfe a Ribas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin G-5 zata iya sulhu da Atiku ana dab da zaɓe?

Game da yuwuwar samun masala da Atiku a lokacin da ake dab da zaɓe, Wike ya ce:

"Ba wannan zance, ba zamu yi sulhu ba, lokaci ya ƙare. Mun faɗa tun ba yau ba kuma ba wanda ya isa ya yi wani abu kan lamarin a yanzu."
"Sun yi amanna zasu iya samun nasara a zabe mai zuwa ko da kuwa babu mu, saboda haka bani da shirin zama da wani nan gaba kan batun sulhu."

Wike, mamban tawagar gwamnonin G-5, ya ja daga da Atiku Abubakar tun bayan zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An samu mafita: Ana tsaka da shan wahalar Naira, Buhari zai yiwa 'yan Najeriya jawabi

Babbar bukatar G-5 tun farko

G-5 ta ƙunshi fusatattun gwamnonin PDP mafi yawansu daga kudancin Najeriya, su ne, Wike, Samuel Ortom (Benue), Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia), da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu).

Gwamnonin sun kafe kan bukatarsu ta shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus a baiwa ɗan kudu sannan zasu goyi bayan ɗan takarar shugaban ƙasa Atiku.

A wani labarin kuma Jam'iyyar SDP Ta Rushe Tsarinta, Ta Koma Inuwar APC Mai Mulki a Kebbi

Ɗan takarar gwamnan da mataimakinsa, yan takarar Sanata da majalisar tarayya na jam'iyyat SDP reshen Kebbi gaba ɗaya sun koma jam'iyyar PDP.

Gwamna Atiku Bagudu ya yaba da wannan mataki da suka ɗauka inda yace yana da yakinin sun yi jaka ne domin cigaban jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel