Muhimman Dalilai Uku da Suka Ja Na Shiga Tallata Tinubu, Shugaba Buhari

Muhimman Dalilai Uku da Suka Ja Na Shiga Tallata Tinubu, Shugaba Buhari

  • Daga karshe shugaba Buhari ya bayyana muhimman dalilai uku da suka ja ya shiga tawagar kamfen Tinubu
  • Shugaban kasa ya ja tawagar APC sun kai ziyarar neman tabarruki fadar mai martaba Sarkin Musulmai dake Sakkwato
  • Bola Tinubu ya fada wa Sultan cewa ya shiga tseren zama shugaban kasa ne domin ya ci nasara

Sokoto - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya faɗa wa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, cewa ya shiga jirgin kamfen Bola Tinubu ne saboda abu uku.

Buhari ya bayyana haka ne yayin ya jagoranci tawagar kamfen shugaban kasa na APC zuwa fadar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato domin neman tabarruki, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ziyarar tawagar APC fadar Sultan.
Muhimman Dalilai Uku da Suka Ja Na Shiga Tallata Tinubu, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Shugaban ƙasa ya ce tawagar yakin neman zaben ta ziyarci fadar Basaraken ne domin neman goyon bayan Sultan kuma ya zabi shiga cikin kamfen ne bisa dalilai uku.

Kara karanta wannan

Ina son gaje kujerar Buhari: Tinubu ya nemi goyon bayan sarkin Musulmi, sarkin ya ba shi amsa

Wane dalilai suka ja Buhari ya shiga kamfen Tinubu?

A jawabinsa, shugaɓan kasan ya ce shi da Bola Tinubu sun jima tare da juna a matsayin abokai tsawon shekaru 20, sannan abu na biyu ya yi abun a yaba lokacin yana gwamnan Legas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Dalili na uku shi ne Tinubu ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na APC a sahihi kuma ingantaccen zaɓe, bisa haka ya zama halastaccen ɗan takara a jam'iyyata."

Daga nan kuma ya bukaci mai Alfarma Sarkin Musulmi da ya goyi bayan Tinubu, wanda Sultan da kansa ya kira da, "Jagaban duniya."

"Na zo nan ne na roki ka marawa dan takararmu baya kuma na san cewa zaka ci gaba da goyon bayanmu," inji Buhari.

Na shiga takara ne domin nasara - Tinubu

Tun da fari, mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar APC, Bola Tinubu, ya faɗa wa Sarkin Musulmai cewa ya shiga tseren kujera lamba ɗaya ne domin ya ci nasara.

Kara karanta wannan

Buhari a Sokoto: Tinubu ya Matukar Fahimtar Matsalolin Najeriya, Ku Zabe Shi

Jaridar Punch ta rahoto Tinubu na cewa:

"Babbar daraja ce zuwa nan musamman tare da rakiyar mai girma shugaban ƙasa muka kawo ziyara fada. Kun riga kun sani amma bari na maimaita, mun zo nan ne domin a gabatar ni a matsayin ɗan takarar APC."
"Mun san cewa baka tsoma baki a siyasa amma dole mu girmamaka idan muka shigo garin na yin kamfe."

Rikici na kara tarwatsa jam'iyyar PDP

A wani labarin kuma Kwamishinoni 11 Sun Fice Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC a Jihar Taraba

Yayin da ake raɗe-raɗin mataimakin gwamnan Sakkwato ya koma APC, rahoto daga Taraba ya nuna cewa akalla kwamishinoni 11 ne suka fice daga PDP.

An tattaro cewa kwamishinonin sun shirya shiga APC a hukumance yayin da jirgin kamfen Tinubu/Shettima ya dira jihar nan da awanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel