Sokoto: Buhari ya Jaddada Cewa Tinubu ya Fahimci Najeriya Sosai, Zai yi Mulki Nagari

Sokoto: Buhari ya Jaddada Cewa Tinubu ya Fahimci Najeriya Sosai, Zai yi Mulki Nagari

  • Shugaban kasa Buhari ya ce zai cigaba da yiwa Tinubu kamfen saboda ya matukar fahimtar Najeriya, sannan ya na gayan bayan jama'a ba tare da duban inda suka fito ba
  • Ya fadi hakan ne yayin jawabi a fadar Sarkin Musulmai, Sa'ad Abubukar a jihar Sakkoto, inda ya roki mutane su kada kuri'unsu ga 'dan takarar shugaban kasar APC
  • Shugaba Buhari yace babu ko shakka Tinubu zai ciyar da kasar nan gaba a fannin tsaro da tattalin arzikin Najeriya

Sokoto - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ya ke so 'yan Najeriya su kada wa 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, Bola Tinubu, saboda yadda yai matukar fahimtar kasar.

Buhari a Sokoto
Sokoto: Buhari ya Jaddada Cewa Tinubu ya Fahimci Najeriya Sosai, Zai yi Mulki Nagari. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Buhari, wanda ya yi jawabi a fadar Sa'ad Abubukar, Sarkin Musulmai, ranar Alhamis, inda ya ce Tinubu na mara wa mutane baya ba tare da dubi da bambancin addini ko kabilarsu ba.

Kara karanta wannan

Ina son gaje kujerar Buhari: Tinubu ya nemi goyon bayan sarkin Musulmi, sarkin ya ba shi amsa

Kamar yadda takardar da Abdulaziz Abdulaziz, hadimin Tinubu ya bayyana, shugaban kasar ya kara da cewa Tinubu mutuminsa ne, wanda ya nuna goggewa a mulki.

"Ya fahimci Najeriya matukar, kuma a koda yaushe yana karfafa mutane daga ko ina a Najeriya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Kamar yadda shugaban kasar ya fada wa Sultan.

"Naje tare da shi Nasarawa da Katsina yanzu gani tare da shi a nan yau. Kuma zan tafi tare da shi sauran wurare. Shi ne 'dan takarar jam'iyyarmu. Shi ne zakaran gwajin dafin zaben fidda gwanin da muka yi. Don haka muka rufa masa baya a matsayin mai rike da tutar jam'iyyarmu."

- A cewarsa.

"Mun zo ne don neman goyon baya da taimako. Ina da tabbacin zamu samu duk taimakon da mike bukata."

- A cewarsa.

Tinubu, yayin jawabinsa na kamfen, ya yi alkawarin shawo kan matsalar tsaro gami da bunkasa ayyukan noma a fadin kasar, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Sarkin Musulmi Abu 3 da Suka Sa Ya Shiga Kamfen Tinubu

Ya kara da cewa zai tabbatar wa jama'a zai iya jagorantar kasar idan aka zabe shi shugaban kasa.

Ayu ya daki Kwano, Yace PDP ta janyo abun kunya

A wani labari na daban, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya bayyana cewa jam'iyyar PDp ta tafka abun kunya.

Yayi wannan subul da bakan ne yayin da yake wa Atiku Abubakar kamfen a jihar Kano yayin da suke gangamin yakin neman zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel