Kwamishinoni 11 Sun Fice Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC a Jihar Taraba

Kwamishinoni 11 Sun Fice Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC a Jihar Taraba

  • Wani rahoto ya ce kwamishinoni 11 a jihar Taraba sun sun fice daga jam'iyar PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya
  • Wannan ci gaban na zuwa ne awanni kaɗan bayan jita-jita ta yawaita kan sauya shekar mataimakin gwamnan Sakkwato
  • Ga dukkan alamu siyasa ta ƙara daukar ɗumi a arewacin Najeriya kwanaki 16 gabanin zaben shugaban ƙasa

Taraba - Rahotanni daga jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya sun nuna cewa Kwamishinoni 11 sun fice daga jam'iyar PDP sun koma APC mai mulkin ƙasa.

Jaridar Punch tace wannan ci gaban na zuwa ne yayin da APC ke shirye-shiryen gangamin ɗan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, da mataimakinsa, Kashim Shettima.

Sauya sheka a Taraba.
Kwamishinoni 11 Sun Fice Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC a Jihar Taraba Hoto: punchng
Asali: UGC

Ana tsammanin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ne da kansa zai karɓi masu sauya shekar zuwa inuwar APC a wurin ralin yakin neman zaben Tinubu na Taraba.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Jam'iyyun Adawa 29 Sun Yanke Shawara, Sun Faɗi Wanda Zasu Marawa Baya Tsakanin Tinubu da Atiku

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa kwamishinonin sun yanke shawarin sauya sheka ne yayin da ya rage kwanaki 16 gabanin zaɓen shugaban kasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da ake jita-jitar mataimakin gwamnan jihar Sakkwato, Manir Ɗan'iya, ya koma APC amma daga baya ya fito ya musanta.

Daily Trust ta ruwaito cewa Daraktan yaɗa labarai na ofishin mataimakin gwamnan, Aminu Abubakar, ya ce uban gidansa ya yi fatali da raɗe-raɗin ya fice daga PDP..

Abubakar ya ƙara tabbatar da cewa mataimakin gwamnan na nan a matsayin mamban PDP kuma ɗan takarar Sanatan jam'iyyar a babban zabe mai zuwa.

Bugu da ƙari, ya yi kira ga magoya bayansa musamman mambobin PDP mai mulkin Sakkwato su yi watsi da wasikar da ake yaɗawa wacce ya kira da murabus ɗin 'yan adawa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamnan CBN, Tambuwal da Bagudu Kan Karancin Sabon Kuɗi, Bayanai Sun Fito

Lamarin dai ya zo da ruɗani domin an ji jagoran APC na jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Wamakko ya sanar da sauya sheƙar Ɗan'iya a wurin ralin Tinubu wanda Buhari ya halarta.

Jam'iyyun adawa 29 a Legas sun koma bayan Tinubu

A wani labarin kuma Bola Ahmed Tinubu ya kara samun gagarumin goyon baya daga jam'iyyu 29 ana gab da zabem 2023

Gamayyar jam'iyyun siyasa 29 sun yanke shawarar yin aiki domin cika burin tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A cewar shugaban jam'iyyun, ɗan takarar shugaban kasa na APC ya yi an gani lokacin da ya mulki jihar Legas tsawon shekaru 8.

Asali: Legit.ng

Online view pixel