Tinubu da Buhari Sun Gana da Sarkin Musulmi, Sun Nemi Goyon Bayansa a Zaben Bana

Tinubu da Buhari Sun Gana da Sarkin Musulmi, Sun Nemi Goyon Bayansa a Zaben Bana

  • Sarkin Musulmi a Najeriya ya gana da Buhari da Tinubu a fadarsa, sun fada masa gaskiyar abin da ya kawo su jihar Sokoto
  • Tinubu ya yi taron gangamin kamfen dinsa a jihar Sokoto, ya roki goyon bayan sarkin Musulmi kan burin gaje Buhari
  • Sarkin Musulmin ya yi martani, ya bayyana matsayarsa game da siyasa da kuma ‘yan takarar da ke zuwa wurinsa a baya-bayan nan

Jihar Sokoto - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya fadawa sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III abin da shugaba Buhari yake so a yi a zaben 2023.

A cewar Tinubu, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana son ya gaje shi ya zama shugaban kasa bayansa a zaben 2023.

Daga nan ne ya tambayi sarkin cewa, shin zai goyi bayansa game da burin Buhari ne ko kuma zai kalubalanci hakan, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Sarkin Musulmi Abu 3 da Suka Sa Ya Shiga Kamfen Tinubu

Tinubu ya nemi goyon bayan sarkin Musulmi
Buhari Yana So Na a Ci Zabe, Shin Za Ka Ki Amincewa da Bukatarsa? Tinubu Ya Tambayi Sarkin Musulmi | Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Ina son gaje Buhari, meye ra'ayinka? Tinubu ga sarkin Musulmi

Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara fadar sarkin kafin wucewar filin wasanni na Gigiya da ke Sokoto don gudanar da taron gangamin kamfen dinsa a can.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Tinubu:

“Mun zo nan ne domin neman goyon bayanka da sanya albarkarka; muna son cin wannan zaben.
“Mun zo ne don a nuna mu a wajenka a matsayin ‘yan takara. Shugaban kasa kuma shugaban sojin kasa Muhammadu Buhari yana tare damu da kansa don yin hakan, Ina son cin zaben nan. Shin akwai wata hanya da za ta sa ka kin amsa bukatar shugaban kasan?

Shi ma da yake magana, shugaba Buhari ya ce:

“Bukata ta goyon bayanka da sanyawar albarkarka; muna son ya ci zabe.”

Martanin sarkin Musulmi

Da yake martani ga bukatar Tinubu da Buhari, sarkin Musulmi ya ce shi ba ya tsoma baki a siyasa balle ya fadi wanda yake goyon baya.

Kara karanta wannan

Buhari a Sokoto: Tinubu ya Matukar Fahimtar Matsalolin Najeriya, Ku Zabe Shi

Ya kuma bayyana cewa, kofarsa da fadarsa a bude take ga kowa da yazo neman addu’a da albarkarsa a matsayinsa na shugaban al’umma, rahoton Channels Tv.

Ya shaidawa Buhari cewa, ‘yan takara da yawa sun zo fadarsa da irin wannan bukatar, ya kuma shaida masu matsayarsa game da siyasa.

Sai dai, ga abin da ya fada game da zaben bana:

“Za mu ci gaba da yiwa kasarmu addu’a. Ba za mu gaji da yin addu’a ba kuma za mu ci gaba da fafutukar wanzar da zaman lafiya da zabe cikin lumana ga kasarmu.”

A wurin taron gangami, Buhari ya ce Tinubu ne dan takarar shugaban kasan da ya fahimci halin da Najeriya ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel