Mata Sun Cika Wajen Gangamin Bola Tinubu, Matar Shugaban Kasa ba ta Iya Zuwa ba

Mata Sun Cika Wajen Gangamin Bola Tinubu, Matar Shugaban Kasa ba ta Iya Zuwa ba

  • Tawagar matan da ke yakin neman zabe a jam’iyyar APC sun yi gagarumin taron kamfe a Kalaba
  • Zahra Buhari ta wakilci Aisha Buhari a taron, amma an ga fuskokin Remi Tinubu da Nana Shettima
  • Matan sun kai ziyara zuwa fadar Edidem Ekpo Okon Abasi Otu V, sun yi kira da a zabi APC a 2023

Cross River - Mutane da-dama suka fita ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba 2022 zuwa babban gangamin matan APC na yankin Kudu maso kudu.

Jaridar Punch tace an yi wannan babban taron yakin neman zabe na Bola Tinubu ne a filin wasan U.J Esuene a garin Kalaba da ke jihar Kuros Riba.

Matar ‘dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar APC, Oluremi Tinubu ta halarci gangamin tare da mai dakin Kashim Shettima, Nana Shettima.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Jingine Siyasa, Ya Bayyana Mutumin Da Ya Cancanci Zama Shugaban Kasa a 2023

Taron ya samu halartar matan manyan ‘yan siyasa a Najeriya, amma jagorar tafiyar mata, Aisha Buhari ba ta iya zuwa ba, sai dai ta aika da wakilci.

Zahra Buhari-Indimi ta wakilci Mahaifiyarta

Zahra Buhari-Indimi ta wakilci Mahaifiyarta a garin Kalaba dauke da gwagwaro mai tambarin APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton yace tawagar ta ziyarci Mai martaba Obong na Kalaba, Edidem Ekpo Abasi Otu V inda ta kai masa ziyarar ban girma kamar yadda aka saba.

Gangamin Bola Tinubu
Matan APC a wajen kamfe Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

A madadin uwargidar shugaban Najeriya, Zahra Buhari-Indimi ta gabatar da jawabi tana mai fatan matasa da mata su kawowa APC nasara a zaben badi.

A zabi APC a 2023

Aisha Buhari take cewa jam’iyyarsu ta tsayawa zaman lafiya da cigaba, don haka tayi kira ga duk wani matashi da wata mace su taya su yakin neman zabe.

Ita kuwa Sanata Oluremi Tinubu, ta yabawa matan Kudu maso kudancin Najeriya, tayi alkawari za a kula da matasalar mata idan aka zabi mai gidanta.

Kara karanta wannan

Mashawarcin Gwamnan Arewa Na Musamman, Shahararren Jigon PDP, Sun Koma APC Gabanin Babban Zaben 2023

Leadership ta fitar da rahoto cewa shugabar matan jam’iyyar APC ta kasa, Dr. Betta Edu wanda mutumiyar jihar ce,tayi kira ga mata su mara masu baya.

Uwargidar gwamnan Kuros Riba, Dr. Linda Ayade tana wajen a yayin da aka rabawa mata tutoci.

2023: Ba a maganar APC - Tsohon SGF

A hasashen da ya yi, Injiniya Babachir David Lawal yace ba a maganar Bola Tinubu da Jam’iyyar APC a wadanda za su iya cin zaben shekara mai zuwa.

Amma Festus Keyamo yana tunkaho da Gwamnonin Jihohi, ‘Yan majalisar tarayya da kwararren ‘dan takarasu a cikin dalilan da za su ba APC nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel