Mashawarcin Gwamnan Arewa Na Musamman, Shahararren Jigon PDP, Sun Koma APC Gabanin Babban Zaben 2023

Mashawarcin Gwamnan Arewa Na Musamman, Shahararren Jigon PDP, Sun Koma APC Gabanin Babban Zaben 2023

  • PDP ta rasa manyan jiga-jigan mambobinta inda suka koma APC a jihar Sokoto gabanin babban zaben 2023
  • Bello Malami, masahawarci na musamman ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, da Alh. Umaru Chori Sanyima, wani jigon PDP, sun koma APC a ranar Asabar, 26 ga watan Satumba
  • Malami ya ce ya fita daga PDP ya koma APC saboda yadda jam'iyyar ke samun karbuwa a jihar Sokoto

Jihar Sokoto - Bello Malami, mashawarci na musamman ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya fita daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben 2023.

Malami wanda ke kula da Marshall, hukumar tsaro na jihar, ya yi bayanin cewa ya shiga APC saboda yadda ta ke samun karbuwa a jihar, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Tambuwal
Mashawarcin Gwamnan Arewa Na Musamman, Shahararren Jigon PDP, Sun Koma APC Gabanin Babban Zaben 2023. Hoto: Ofishin Gwamnatin Jihar Sokoto.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PRP Ta 'Rushe' A Sokoto, Dukkan Yan Takarar Ta Sun Koma APC

Jagoran APC a jihar kuma sanata mai wakiltar Sokoto North, Aliyu Magatakarda, Wamakko da Ministan Harkokin Yan Sanda, Muhammad Maigari Dingyari, suka tarbe shi a tsohuwar gidansa da ke Gawon Nama a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba.

Zan yi aiki don nasarar APC a zaben 2023

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon hadimin Gwamna Tambuwal din ya yi alkawarin yin aiki don nasarar jam'iyyar APC yayin zaben da ke tafe.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, da ya ke magana a wurin taron, dan takarar gwamna na APC a jihar, Ahmad Aliyu, ya ce Malami ya dawo gida ne daga bakunta da ya tafi.

Ya ce:

"Ka dawo inda za a daraja ka tare da girmama ka. Kamar yadda ka sani mu a APC ba mu nuna fifiko tsakanin mambobin mu kuma muna daraja su."

Zaben 2023: Jam'iyyar PRP Ta Yi Maja Da APC a Jihar Sokoto

Kara karanta wannan

A Karon Farko Mataimakin Gwamnan Sokoto Ya Magantu Kan Sauya Sheka Zuwa APC

Hakazalika, kun ji cewa yan watanni kafin babban zaben shekarar 2023, jam'iyyar PRP a jihar Sokoto ta yi maja da babban jam'iyyar hamayya ta APC a jihar.

Dukkan yan takarar da ke karkashin jam'iyyan ta PRP da jiga-jiganta sun dunguma sun koma jam'iyyar ta APC ciki har da Sai'idu Muhammad Gumburawa dan takarar gwamna na PRP a jihar.

Wadanda suka sauya shekar sun ce sun dauki wannan matakin ne domin bada gudunmawarsu don kawo cigaba a jiharsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel