Gwamna Ayade Ya Bayyana Dan Takara Daya Tilo Dake da Gogewar Zama Magajin Buhari a 2023

Gwamna Ayade Ya Bayyana Dan Takara Daya Tilo Dake da Gogewar Zama Magajin Buhari a 2023

  • Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba yace Bola Tinubu da Shettima sun kere sauran yan takara cancanta da shugabancin Najeriya
  • A wurin gangamin mata na kudu maso kudu a Kalaba, Ayade yace Tinubu ya nuna kwarewa a tarin siyasarsa
  • Aisha Buhari, shugabar kwamitin matan APC, tace tana da kwarin guiwa mata ba zasu kauce wa Tinubu ba a 2023

Calabar, Cross River - Gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade, ya ware ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC, ya ayyana shi da mafi gogewa a cikin 'yan takarar 2023, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gwamnan yace Bola Tinubu da Kashim Shettima sun fi kowa cancanta su karbi ragamar Najeriya bisa la'akari da ƙalubalen da ake fama da su sakamakon rikice-rikicen duniya.

Gangamin matan APC a Kalaba.
Gwamna Ayade Ya Bayyana Dan Takara Daya Tilo Dake da Gogewar Zama Magajin Buhari a 2023 Hoto: thenation
Asali: UGC

Ben Ayade ya yi wannan furucin ne a wurin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na matan APC wanda ya gudana a filin wasan U.J Esuene, Kalaba, babban birnin Kuros Riba a karshen mako.

Kara karanta wannan

Magajin Buhari: Mata da Matasa Zasu Tara Wa Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa Kuri'u Miliyan 40 a 2023

A wata sanarwa da kakakin kwamitin kamfen matan APC, Rinsola Abiola, ta fitar ranar Lahadi, gwamnan ya yaba da kwarewa da kamalan ɗan takarar shugaban ƙasa na APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi ga dandazon matan da suka taru a gangamin Kudu maso kudu da ya ƙunshi jihohi shida, Gwamna Ayade ya ce:

"Muna son Bola Tinubu ba wai don gogewarsa ba, muna goyon bayansa ne saboda ya nuna zai iya a tarihi, mutum ne da zai haɓaka arzikin da ake samu yanzu, ya kawo cigaba kana ya ɗaga martabar ƙasarmu."
"Takarar Tinubu da Shettima ta haɗa kwararru kuma gogaggu kuma sune haɗin da zasu iya kawo mana cigaban da muke mafarki a cikin waɗanda suka shiga neman kuri'a."

Uwar gidan shugaban ƙasa kuma jagoran kwamitin mata, Aisha Buhari, wacce ta samu wakilcin ɗiyarta, Zahra Buhari Indimi, ta bayyana kwarin guiwarta kan mata a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Jihar Kano Da Wasu Jihohin Arewa 5 Da Nike Da Tabbacin Zan Lashe: Tinubu

Tace APC ta shiya tsaf don ci gaba da zuba wa al'umma ayyuka da zaman lafiya, ta kuma roki matan da su sadaukar da kansu a kamfen ɗan takarar APC, kamar yadda Tribune ta rahoto.

A wani labarin kuma Tinubu Ya Kara Karfi a Arewa Yayin da wasu Jiga-Jigai da Wasu Yan Takarar Majalisa Sun Koma APC

Manyan jiga-higar da suka haɗa tsoffin kwamishinoni da 'yan takara a jam'iyyun PDP, SDP, ADC da sauransu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar Kwara.

Gwamna jihar, Abdurrahman AbdulRazaq, yayin yi wa masu sauya sheƙar maraba, ya ce jam'iyyar PDP ta zama kwanko babu kowa a cikinta sai yan soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel