Abubuwa 5 da Za Su Jawo Tinubu Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa - Ministan Buhari

Abubuwa 5 da Za Su Jawo Tinubu Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa - Ministan Buhari

  • Babachir David Lawal ya yi wani fashin baki da ke nuna ba a lissafi da Bola Tinubu a ‘yan takaran 2023
  • Tsohon Sakataren gwamnatin yace APC ba ta da kuri’un Kiristoci da kuma mutanen Arewacin Najeriya
  • Kakakin kwamitin yakin neman zaben APC, Festus Keyamo yana ganin shirita ce Babachir Lawal yake yi

Abuja - A ra’ayin Babachir David Lawal, babu ta yadda za ayi jam’iyyar APC mai mulki ta cigaba da rike madafan iko bayan watan Mayun 2023.

A wata hira da aka yi Injiniya Babachir David Lawal a gidan talabijin Channels a ranar Alhamis, 24 ga Nuwamba, yace APC ba za ta ci zabe ba.

Shi Babachir David Lawal yana ganin Peter Obi ne zai yi nasara a zaben shugaban kasa, amma duk da haka yace za a iya zuwa zagaye na biyu.

Kara karanta wannan

2023: Tun da ‘Dan takaransa ya sha kashi, Buratai ya nuna wanda yake goyon baya

A lokacin da zaben zai shiga zagaye na biyun, Babachir Lawal yana ganin cewa ba a maganar ‘dan takara watau Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC.

Babu nan - babu can ga Tinubu?

‘Dan siyasar yace tikitin Musulmi da Musulmi da Bola Tinubu ya dauko zai jawo masa fushin duk wani Kirista har a wajenArewacin Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon Sakataren gwamnatin ya kara da cewa Tinubu ba zai iya doke Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso a jihohin Arewacin kasar ba.

Lawal yace APC ta dogara ne da wasu mutane da ba abin dogara ba ne a zaben shugaban kasan badi. Amma ba kowa ya yarda da batunsa ba.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Atiku Abubakar Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Babu 25% a jihohi da-dama

Jihohin da Lawal yake ganin jam’iyyarsa ba za ta samu ko da 25% sun hada da; Kebbi, Sokoto, Nasarawa, Zamfara, Yobe, Adamawa, da irinsu Gombe.

Kara karanta wannan

Barakar Tashin Hankali Ta Kunno Kai a Tafiyar Yakin Neman Zaben Peter Obi a 2023

An ji Lawan a hirar da aka yi da shi yana cewa Tinubu ba zai samu daya bisa hudun kuri’un da mutane za su kada Taraba, Filato da Benuwai ba.

Martanin Festus Keyamo

Festus Keyamo ya na ganin akwai abin ban mamaki tattare da maganar Babachir, yace APC tana da gwamnoni da rinjayen da zai ba ta nasara.

“‘Ya ‘yan jam’iyya masu rajista mutum miliyan 40, Gwamnoni masu-mulki 22, rinjaye mai karfi a majalisar tarayya, ‘dan takaran da a ashekaru 23 ba ayi Gwamnan da ya fi shi ba.
Sanna ga asalin jam’iyyar hamayya tana cikin rikici da Gwamnoni biyar. Kuma a ce babu maganar APC a zaben zagaye na biyu. Magana mafi ban mamaki da aka yi a shekarar 2022.”

- Festus Keyamo

APC ce amsar - Tukur Yusuf Buratai

An samu rahoto Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya ya fadi wanda ya dace da mulki da Gwaninsa, Rotimi Amaechi ya gaza samun tikiti.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Buratai yana goyon bayan Bola Tinubu ya gaji mulki daga hannun Muhammadu Buhari saboda a cigaba da ayyukan da aka fara musamman a Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel