Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke, An Yi wa Kauyuka 10 Kaca-kaca a Jihar Kano

Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke, An Yi wa Kauyuka 10 Kaca-kaca a Jihar Kano

  • An samu rashin kwanciyar hankali a wasu kauyuka da ke karkashin karamar hukumar Minjibir a Kano
  • Ana zargin wasu makiyaya da shiga gonakin Bayin Allah suka yi barna, sannan su ka aukawa manoman
  • Kungiyar Miyetti-Allah tace mutane sun yi shuka ne a kan hanya, hakan ya jawo dabbobi suka yi barna

Kano - Akalla mutum biyu sun hallaka baya ga mutane da-dama da suka samu rauni a dalilin fada da ya kaure a karamar hukumar Minjibir a jihar Kano.

Wani rahoto mara dadi da ya fito daga Daily Trust ya bayyana cewa an rigima ta shiga tsakanin wasu makiyaya da kuma manoma a kauyen Minjibir.

Ana tunanin kauyuka kusan 10 aka yi wa barna, aka lalata gonakin jama’a a dalilin takaddamar.

Daga lokacin da rikicin nan ya barke zuwa yanzu, kauyukan da abin ya shafa sun hada da Daurawa, Kuka Bakwai, Geza, Macinawa da kuma Kasakore.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga Sun Halaka Mutum 2, Sun Tarwatsa Kauyuka 10 a Kano

An yi wa manoma asara

Wani wanda ya bada labarin abin da ya auku, yace a karshen makon jiya wasu makiyaya suka saki dabbobinsu a gonakin da ake shirin girbewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda rahoton ya zo, makiyayan sun kashe mutane biyu mazauna garin da suka tunkare su.

Makiyaya da Manoma
Wani makiyayi da dabbobinsa Hoto: www.theguardian.com
Asali: UGC

Idi Lawan wanda mazaunin karamar hukumar ne, yace makiyayan sun kashe ‘danuwansa, Sunusi Usman bayan dabbobinsu sun lalata masa wake.

Da ya je gonar wakensa, Sunusi Usman ya fahimci an yi masa barna, sai ya je wajen masu dabbobin domin ya kai kuka, a nan waninsu ya harbe shi da baka.

Shi kuma wani manomi yace ya hangi dabbobi na cinye masa gyada, don haka sai ya bukaci su bar masa gona, amma a karshe suka yi masa rauni a jiki.

Inda matsalar ta ke - MACBAN

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Abin Fashewa Ya Yi Mummunar Ɓarna A Babban Kasuwa A Najeriya

Basiru Dauda Kunya mutumin yankin ne, ya shaidawa manema labarai tun shekarar bara ake yi masu irin wannan barna, a karshe abin ya kai ga haka.

Kungiyar MACBAN wanda aka fi sani da Miyetti-Allah tace manoman sun yi shuka a kan hanyar wucewa ne, hakan ya jawo dabbobi suka yi masu barna.

Hajiya Aisha Muhammad ta kungiyar, ta zargi wani shugaban karamar hukuma da saidawa mutane hanyar dabbobi, su kuma suka maida su wajen noma.

'Yan sanda sun yi magana

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma yace yanzu abubuwa sun lafa. Jami’in yace rundunar ‘yan sandan tana yin bincike.

Premium Times tace mutum daya aka tabbatar da ya mutu, daya yana asibiti.

Ambaliyar ruwa za ta ci Minista

‘Yan Majalisar Wakilai daga jihohin Bayelsa, Ribas, Delta, Cross River, Edo da Akwa Ibom ba su ji dadin maganar da Ministar jin kai tayi kwanakin baya ba.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Hargitsa Kauye, Sun Yi Awon Gaba da Basarake da Mutanen Gari

An ji labari Sadiya Umar Farouq tace a duk inda aka yi ambaliya babu inda abin ya yi kamari irin jihar Jigawa, 'yan majalisa sun zargi Ministar da son-kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel