NPC: Gurabe Miliyan 2 Suna Jiran Mutane, Gwamnatin Tarayya Za Ta Dauki Aiki a 2023

NPC: Gurabe Miliyan 2 Suna Jiran Mutane, Gwamnatin Tarayya Za Ta Dauki Aiki a 2023

  • Hukumar kidaya ta kasa ta NPC tace mutane miliyan biyu za ta tanada domin suyi mata aiki a 2023
  • A shekara mai zuwa, gwamnati za tayi kidaya domin sanin adadin mutanen da ke rayuwa a Najeriya
  • Kwamishinan NPC na Ekiti, Ayodeji Ajayi ya yi karin bayani game da tsare-tsaren da hukumar take yi

Ekiti - Hukumar kidaya ta kasa watau NPC tace mutane miliyan biyu za a dauka haya a Najeriya domin suyi aikin kidayar ‘yan kasa a shekarar 2023.

Hukumar ta fara da jan-kunnen ma’aikatan da za a dauka cewa ka da suyi abin da zai bata mata suna. This Day ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis.

Duk wanda aka samu da laifi ko rashin gaskiya wajen aikin kidayar nan da za ayi, zai fuskanci fushin hukuma, za a hukunta har wanda ya tsaya masa.

Kara karanta wannan

Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke, An Yi wa Kauyuka 10 Kaca-kaca a Jihar Kano

Domin ganin an yi adalcin daidaita tsakanin jinsi wajen daukar aikin, Kwamishinan NPC na Ekiti, Ayodeji Ajayi yace mata za su samu gurabe akalla 40%.

Ayodeji Ajayi ya yi wannan bayani da ya zanta da manema labarai jiya a garin Ado Ekiti.

Kamar yadda Vanguard ta rahoto, kwamishinan na NPC yace mutane miliyan biyu aka yi tanadi domin su gudanar da wannan muhimmin aiki a badi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Yan NPC
Masu aikin kidaya a 2006 Hoto: www.dataphyte.com
Asali: UGC

Ajayi yace wadanda za su kirga adadin mutanen Najeriyan sun hada da asalin ma’aikatan NPC da wasu da za a dauka haya domin aikin wucin gadi.

Za a samu horo da satifiket

Tsohon shugaban ma’aikatan jihar na Ekiti yace za a horas da wadanda za su yi aikin kidayar.

Duk wani matashi da ya yi aikin da kyau, kuma aka ga kokarinsa, zai samu takardar shaida daga NPC wanda zai taimaka masa wajen samun aiki nan gaba.

Kara karanta wannan

Manoma sun huta, sojoji sun sheke wani kasurgumin shugaban 'yan bindiga a Zamfara

Hukumar tana harin ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jihohi da sauran mutanen Najeriya masu nagarta da gaskiya domin cike guraben aikin da za a samu.

Rahoton yace za a bukaci malaman firamare, sakandare da manyan makarantu musamman kwararru a ilmin kasa da na halayyar ‘Dan Adam da kidaya.

A baya an rika amfani da takardu ne don haka aka rika fitar da alkaluman bogi, wannan karo da na’urorin zamani za ayi aiki domin a hana yin magudi.

Siyasar 2023

Dazu ne aka ji tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu yace yana ganin da wahala a samu ‘dan takaran da zai iya doke Bola Tinubu a zaben badi.

Masu fashin bakin siyasa suna ganin cewa wadanda za su kawowa Tinubu kalubale a zaben badi su ne; Atiku Abubakar, Peter Obi sai Rabiu Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel