An Gano Budurwar da Fada Tekun Legas Jami'ar Hukumar Tsaron Farin Kaya ce

An Gano Budurwar da Fada Tekun Legas Jami'ar Hukumar Tsaron Farin Kaya ce

  • Kashe kai dai a Nigeria ya Zama Bakon Al'amari da ba kasafai a kanji an yi ba, kamar yadda ake ji a sauran kasashen duniya.
  • Yan mata dai na zargin samari basa musu adalci musamman a wajen neman su da aure ko kuma yayin soyayya.
  • Jami'an Hukumar (DSS) da Jami'an Sa kai da Jami'an Hukumar kashe gobara na Jihar Lagos Suna Duk mai yiwa dan ganin an gano ta.

Lagos: Budurwar da ta fada tekun legas a ranar alhamis din data gabata an bayyana sunan ta da Adetutu Adedokun, wacce ma’aikaciyar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ce.

Majoiyoyi sun bayyana cewa budurwa, wadda ta gaji sahun mahaifanta, jami'ar hukumar ce masu amfani da fararen kaya wajen bayar da bayannan sirri da takile rikici.

Kara karanta wannan

Muna sane: IGP ya fadi matakin da 'yan sanda ke dauka bisa harin da aka kai kan tawagar Atiku

Budurwar da ta fada teku
An Gano Budurwar da Fada Tekun Legas Jami'ar Hukumar Tsaron Farin Kaya ce Hoto: Channels tv
Asali: UGC

A ‘yan watannin da suka gabata, Adedokun wacce ta wuce shekara 30, ta samu wasikar yabo daga babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS a matsayin ta na ‘Jami'ar da tai fice wajen aiki a kayan gida kamar yadda kafar Channels Tv suka Ambato.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adetutu ta cika shekara 30 da haihuwa.

An kuma bayar da rahoton cewa saurayin wanda aka kashe ya nemi aurenta makonnin da suka gabata.

Direban motar Haya da ta hau yace

Na ji suna muhawara ita da wani wanda yakai su da cece kucen daga bisani ta fita da ga motar tare da fadawa tekun

Jim kadan bayan faruwar lamarin dai, jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas, LRT, da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta jihar Legas (LASWA), da jami’an hukumar DSS, suka dauki in da al'amarin ya faru.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Arewa yayin da 'yan bindiga suka sace wani Limamin Katolika

Ba kasafai ba dai aka fiye jin kashe kai a sanadiyyar soyayya ko akasin haka a nahiyar afrika ba. Yawancin abubuwan da suke janyo mutane su kasahe kansu basu fiye matsaltsalo na rashi, bashi ko kuma kuma wani abun kunya da wani ko wata suka aikata ba aikata ba.

Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, LASEMA, Dokta Olufemi Oke-Osanyintolu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya kuma ce har yanzu jami’an na bincike dan ceto gawarta

Asali: Legit.ng

Online view pixel