Harin da Aka Kai Wa Ayarin Atiku Ya Tabbatar da Irin Halin Takaicin APC Ke Ciki, Inji PDP

Harin da Aka Kai Wa Ayarin Atiku Ya Tabbatar da Irin Halin Takaicin APC Ke Ciki, Inji PDP

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi jiga-jigan APC da kitsa duk wata manakisa ta harin da aka kai kai tawagar dan takarar shugaban kasa na PDP
  • PDP ta ce ta gano yadda wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar APC suka yi hayar 'yan daba domin aiwatar barnar da suka aikata
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin jam'iyyun siyasa a Najeriya, musamman yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa

Najeriya - Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi Allah-wadai da harin da aka kai kan ayarin motocin dan takararta na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a jihar Borno.

Wasu adadi na magoya bayan Atiku sun samu raunuka yayin da wasu 'yan daba suka farmake su a ranar Laraba a Maiduguti, babban birnin jihar Borno.

Channels Tv ta ruwaito cewa, an farmaki tawagar ta Atiku ne jim kadan bayan da ya fito daga gidan sarautan Shehun Borno, inda ya nufi filin gudanar da taron gangamin kamfen.

Kara karanta wannan

Abin ya fara yawa: Ni da Masoyana Na Fuskantar Hadari Daga APC - Atiku Ya Koka

PDP ta caccaki PDP kan yadda aka farmaki tawagar Atiku a Borno
Harin da Aka Kai Wa Ayarin Atiku Ya Tabbatar da Irin Halin Takaicin APC Ke Ciki, Inji PDP | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Martanin jam'iyyar PDP

Jim kadan bayan harin, kakakin jam'iyyar PDP, Debo Ologunagba ya fitar da sanarwa tare da yin kira ga sufeto janar na 'yan sanda Usman Alkali Baba da ya kame masu laifin tare da dakile faruwar irin wadannan ayyukan barna a wuraren kamfen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, ya zargi jam'iyyar APC mai mulkin jihar da yin hayar 'yan daba domin dagula lamurran PDP a jihar, tare da cewa jam'iyyar ta APC na cikin takaici da kishin karbuwar PDP.

A bangare guda, ya zargi APC da hasada da yadda dan takarar na PDP ya samu karbuwa a jihar Borno, jihar abokin takarar Bola Tinubu na APC, rahoton PM News.

Sannan, ya shaida cewa, tuni bayanai da PDP ta samu suka gano yadda 'yan APC suka tara 'yan daba domin hargitsa kamfen dan takarar shugaban kasa na PDP a jihar ta Borno.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jam’iyyar PDP ta Bayyana Shirinta Na Hambarar Da APC A Wani Babban Jihar Arewa

An farmaki tawagar Atiku a jihar Borno

Idan baku manta ba, rahotonmu na baya ya bayyana wasu tsagerun 'yan daba suka farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar a jihar Borno.

Akalla mutane 70 ne suka samu raunuka, wadanda tun a lokacin aka mika su asibiti domin duba lafiyarsu da yi musu jinya cikin gaggawa.

Hakazalika, rahoton da muka samo ya nuna cewa, an lalata motoci da dama na 'yan PDP kuma jam'iyyar ta zargi 'yan APC da kitsa duk wata kitimurmura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel