Abin ya fara yawa: Ni da Masoyana Na Fuskantar Hadari Daga APC - Atiku Ya Koka

Abin ya fara yawa: Ni da Masoyana Na Fuskantar Hadari Daga APC - Atiku Ya Koka

  • Atiku Abubakar ya yi tir da harin da ya yi ikirarin ake yawan kai wa tawagarsa a wajen yawon kamfe
  • ‘Dan takaran kujerar shugabancin Najeriyan ya fitar da jawabi ta bakin Paul Ibe a ranar Larabar nan
  • Mr. Paul Ibe yace magoya bayan APC ne suka aukawa tawagar Atiku a babban birnin jihar Borno dazu

Abuja - Atiku Abubakar mai neman zama shugaban Najeriya a 2023 a inuwar jam’iyyar hamayya ta PDP ya koka a kan barazanar da yake fuskanta.

Vanguard tace Alhaji Atiku Abubakar ya fitar da jawabi na musamman ta hannun hadiminsa Paul Ibe bayan harin da ya yi ikirarin an kai masa a yau.

Da yake magana a garin Abuja a ranar Laraba, Mista Paul Ibe yace abin takaici ne wasu su rika kai wa tawagar ‘dan takaran shugabancin kasar hari.

Kara karanta wannan

Ana nan tare: Gwamnan PDP Ya Karyata Rade-Radin Watsi da Tafiyar Atiku Abubakar

Atiku Abubakar ya je garin Maiduguri domin ya yi kamfe, amma sai ga labari cewa ‘yan iskan gari sun aukawa manyan bakin da za su wajen taron PDP.

Aikin 'Yan APC ne ba kowa ba - Atiku

A cewar Mai magana da yawun bakin ‘dan takaran, jama’a da-dama sun halarci taron yakin neman zaben na PDP da aka yi a farfajiyar Ramat Square.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wazirin Adamawa ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da kai masa harin, ya kuma nuna cewa ba wannan ne karon farko da aka yi masa irin wannan ba.

Atiku
Atiku Abubakar da Shehun Borno Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook
“Abin takaici ne da ‘yan jam’iyyar APC na Borno za su dauki hayar mutanenta domin kai hari ga tawagar motocin manyan bakin da kafin nan sun kai ziyara zuwa fadar Shehun Borno.
Duk da za a iya fahimtar cewa wannan mummunan ta’adi karamin aikin 'yan jam'iyyar APC ne, dole ne a tabbatar da cewa a wannan karon, aski ne ya zo gaban goshi.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar PDP Ta Fadi Wanda Atiku Zai Mika Wa Mulki Bayan Gama Wa'adinsa

Dole sai an yi hattara - Ibe

Jam’iyyar APC ta rude da ganin dinbin mabiya da suka zo karbar ‘dan takaranmu na zaben shugaban kasa, sun saki layin damukaradiyya da nufin kora mutane daga wajen taron.
Irin wannan ne abin da ya faru a jihar Kaduna, kuma yana da muhimmanci a ankarar da duk masu ruwa da tsaki wajen shirya zabe mai kyau game da danyen aikin na APC."

- Paul Ibe

A jawabin da ya fitar dazu, an rahoto Ibe yace APC tana yi wa Atiku Abubakar wannan ne musamman a jihohin Arewacin Najeriya, inda ya fito.

Udom Emmanuel ya yi magana

Dazu nan rahoto ya zo cewa Udom Emmanuel yace shi cikakken ‘dan jam’iyya ne mai biyayya, ba zai sauka daga shugabancin kwamitin kamfen PDP ba.

Gwamnan ya nuna sam bai da niyyar bin layin da Seyi Makinde, Nyesom Wike, Okezie Ikpeazu, Samuel Ortom da su Ifeanyi Ugwuanyi suka dauka.

Kara karanta wannan

PDP Tayi Karar ‘Dan Takaran APC a Kotu, Ta Kawo Hujjar da Za ta Iya Hana Shi Mulki

Asali: Legit.ng

Online view pixel