Zaben 2023: Jam’iyyar PDP ta Bayyana Shirinta Na Hambarar Da APC A Wani Babban Jihar Arewa

Zaben 2023: Jam’iyyar PDP ta Bayyana Shirinta Na Hambarar Da APC A Wani Babban Jihar Arewa

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta sanar da cewa za ta tarbi sabbin mambobi miliyan 1 a jihar Borno
  • A cewar jam'iyyar, dukkan sabbin mambobin guda miliyan daya sun shigo jam'iyyar ne cikin wata guda
  • An tattaro cewa mafi yawancin sabbin mambobin sun sauya sheka ne daga jam'iyyar APC mai mulki

Borno, Maiduguri - Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta ce za ta yi kamfen din dan takarar shugaban kasarta a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamban 2022 a Maiduguri, babban birnin jihar.

Kamar yadda Channels TV ta rahoto, jam'iyyar na cike da kwarin gwiwa tana mai cewa dan takarar shugaban kasarta, Atiku Abubakar zai ci galaba a Borno a babban zaben 2023 da ke tafe.

Atiku Abubakar
Zaben 2023: Jam’iyyar PDP ta Bayyana Shirinta Na Hambarar Da APC a Wani Babban Jihar Arewa. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar PDP Ta Fadi Wanda Atiku Zai Mika Wa Mulki Bayan Gama Wa'adinsa

Kakakin PDP, Debo Ologunagba cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai ya yi ikirarin Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ba shi ga magoya baya sosai a jihar Borno duk da cewa jihar na karkashin jam'iyyar APC ne kuma jihar abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima.

Ya kuma lura cewa zai yi wahala Tinubu ya samu kuri'u kashi 25 cikin 100 a dukkan jihohin Najeriya, Leadership ta rahoto.

Ologunagba ya ce:

"A yayin da Asiwaju Bola Tinubu ba tsaran dan takarar PDP bane wanda aka fi kauna da so wato Atiku Abubakar, tuni mutanen Borno sun dawo rakiyar dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, Kashim Shettima saboda gazawarsa a matsayin gwamnan jihar."

Zaben 2023: "Mambobin APC fiye da miliyan daya sun shigo PDP cikin wata guda" - Ologunagba

Ologunagba ya kuma ce jam'iyyar PDP ta samu sabbin mambobi fiye da miliyan daya cikin kwanaki 30.

Kara karanta wannan

Shugaban Masu Rinjaye A Majalisar Wakilai Doguwa Ya Magantu Game Da Batun Sauya Shekarsa Daga APC

Ya bayyana cewa galibin wadanda suka shigo jam'iyyar mambobin APC ne.

Kakakin na PDP ya ce:

"Mutanen Borno sun sha bakar wahala karkashin APC kuma sun kosa su samu sabuwar rayuwa karkashin PDP da Atiku Abubakar wanda kwarewarsa a jagoranci alama ce da ke karfafa musu gwiwar samun tsaro, tattalin arziki, ayyukan more rayuwa da zaman lafiya."

Atiku Yana Da Tambayoyi Da Zai Amsa Kan Alakarsa Da Yan Ta'adda, In Ji Fani-Kayode

A bangare guda, jigon APC Femi Fani-Kayode ya alakanta dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da ta'addanci yana mai cewa akwai bukatar a bincike shi.

Tsohon ministan sufurin jiragen saman ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata 8 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel