Buba Galadima: Buhari Ya Kiyaye, ‘Yan APC Dinsa Na Neman Bata Masa Suna a Ofis

Buba Galadima: Buhari Ya Kiyaye, ‘Yan APC Dinsa Na Neman Bata Masa Suna a Ofis

  • Jagora a NNPP, Buba Galadima yace akwai shirin da ake yi da nufin a hana BVAS amfani a zaben 2023
  • Injiniya Buba Galadima ya shaidawa manema labarai cewa hakan zai bada dama APC ta shirya magudi
  • Tsohon jigon na jam’iyya mai mulki ya ba shugaban kasa shawara ya sa ido da mutanensa da ke APC

Abuja - Injiniya Buba Galadima wanda yana cikin jagororin jam’iyyar NNPP na kasa, yace akwai mugun nufin da ake yi wa hukumar INEC a 2023.

Buba Galadima ya zanta da talabijin Channels TV a ranar Alhamis, 27 ga watan Oktoba 2022, yayi masu fashin bakin yadda siyasa take tafiya.

Fitaccen ‘dan adawar ya zargi wasu mutane a jam’iyyar APC da shirya makarkashiya domin a hana hukumar zabe yin amfani da na’urorin zamanin.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Kabiru Gaya Ya Ci Taliyar Karshe a Majalisar Dattawa

A cewar Galadima, ana so Farfesa Mahmud Yakubu ya sauka ko a ki amincewa BVAS suyi aiki, wanda hakan zai jawo jam'iyyar APC tayi magudi.

Akwai wata makarkashiya inji Galadima

"Akwai abubuwan damuwa, har INEC tace ba a cire shugaban hukumar ba, akwai abin lura a nan da mafi yawan ‘yan jarida ba su fahimta ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An taso shugaban INEC a gaba sosai domin ayi wasa da dokar zabe na kasa.
Buhari
Muhammadu Buhari yana kada kuri'a Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Domin APC mai mulki tana neman tilastawa shugaban hukumar INEC ya rubuta takarda ga majalisar tarayya, yace babu dalilin tursasa amfani da BVAS.
Wannan kuma shi ne mafi munin rashin kishin kasa da wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki suke shirin yi.
Ina son shugaban tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari ya sa ido kan wasu bata-gari a jam’iyyar APC da suke neman bata masa suna lokacin da ya bar ofis."

Kara karanta wannan

"Dalilin Da Yasa Cikin Sauki Tinubu Zai Lallasa Atiku, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasan 2023"

- Buba Galadima

Sanata Gaya ya kama kan shi?

"Ku saurari Sanata Kabiru Gaya, shugaban kwamitin INEC, kwanan nan ya je gidan talabijin, yana fadawa Duniya dole sai an ba INEC damar amfani da BVAS

- Buba Galadima

A bidiyon da aka wallafa, Galadima yace dalilin Sanatan shi ne a mazabarsa ta Gaya da ke Kano babu karfin na’urar da za a iya aika sakamakon zabe.

A karshen gabar tattaunawar, yace NNPP ce jam'iyyar da za a buga da ita a 2023.

NANS ta lashe amai?

A baya an ji labari wasu gungun dalibai sun fito suna cewa 'Dan takaran APC watau Bola Tinubu ne zabin daliban Najeriya a zaben shugaban Najeriya.

Daga baya shugabannin NANS; Emmanuel Adegboye, John Alao da Opeoluwa Awoyinfa sun fitar da jawabi, sun ce ba su tsaida ‘dan takara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel