Buba Galadima: Kabiru Gaya Ya Ci Taliyar Karshe a Majalisar Dattawa

Buba Galadima: Kabiru Gaya Ya Ci Taliyar Karshe a Majalisar Dattawa

  • Buba Galadima, tsohon makusancin shugaban kasa Buhari kuma jigo a jam’iyyar NNPP, yace Sanata Kabiru Gaya ya ci taliyar karshe a majalisar dattawan kasar nan
  • Galadima yace Gaya ya kammala shirya yadda za a aiwatar da abinda suka yi niyya a mazabarsa shiyasa yace BVAS ba zata yi aiki a mazabarsa ba
  • Jigon jam’iyyar NNPP yayi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya dage kada wasu su bata masa suna yayin da ya bar ofishinsa

Kano - Jigon jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari, kuma tsohon makusancin Shugaba Muhammadu Buhari, Buba Galadima, yace sanata mai wakiltar mazabar Kano ta kudu, Kabiru Gaya, yana cin taliyarsa ta karshe ne a majalisar dattawa.

Buba Galadima
Buba Galadima: Kabiru Gaya Ya Ci Taliyar Karshe a Majalisar Dattawa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Galadima ya bayyana hakan yayin tattaunawar da aka yi da shi a shirin Siyasa a Yau na gidan talabijin din Channels.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Ya Cigaba da Tallata Bola Tinubu Duk da Shi Yana Goyon bayan Atiku Abubakar

Yace:

“Ku saurari Sanata Kabiru Gaya wanda a baya-bayan nan aka zanta da shi a gidan talabijin inda yake cewa dole ne a bai wa hukumar zabe damar amfani da BVAS ko kada su yi amfani da shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Saboda a mazabarsa ta Gaya, wacce take tsakiyar jihar Kano, babu netwok da za a iya tura sakamakon zabe.
“Kawai yana shirya tabbatar da abinda suka kalla ne saboda sun san cewa sun rasa wannan zaben. Shi karan kan shi ya san taliyar karshe yake ci a matsayin sanata.”

Galadima yace hukumar zabe mai zaman kanta tana cikin takura kan kada tayi amfani da tsarin BVAS don zaben 2023 mai zuwa.

“Ina kira ga shugaban kasar Najeriya da ya kiyaye duk wasu bata-gari dake neman bata masa suna a yayin da ya bar ofishinsa.”

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Kwankwaso Zai Kawo Dukkan Jihohin Arewa a 2023

- Ya kara da cewa.

Buba Galadima: Kwankwaso Zai Kawo Dukkan Jihohin Arewa a 2023

A wani labari na daban, Buba Galadima, tsohon mamba a kwamitin yardaddu na jam’iyyar APC, yace Rabiu Kwankwaso ne zai lashe zabe a dukkan jihohin arewa a zaben shugabancin kasa na 2023 dake zuwa.

Kwankwaso shi ne ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar NNPP mai alamar abarba, The Cable ta rahoto.

A yayin jawabi a ranar Alhamis a tattaunawarsa da Channels TV, Galadima yace Kwankwaso zai lashe zabe a shiyoyi uku na arewa kuma ya samu kuri’u a inda abokan hamayyarsa ke da karfi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel