Murnar Tinubu Za ta Koma Ciki, Daliban Najeriya Sun Karyata Batun Goyon Bayansa

Murnar Tinubu Za ta Koma Ciki, Daliban Najeriya Sun Karyata Batun Goyon Bayansa

  • Shugabannin NANS na jihohin Yarbawa sun ce ba suyi wa wani ‘Dan takaran 2023 mubaya’a tukuna ba
  • Kungiyar daliban tace sai ta duba manufofin masu neman zama shugaban kasa, sai ta dauki matsaya
  • A baya an ji labarin wasu dalibai na cewa Bola Tinubu da Kashim Shettima na APC za su ba kuri’arsu

Lagos - Kungiyar daliban Najeriya watau NANS na shiyyar Kudu maso yamma ta nesanta kan ta daga maganar yi wa wani ‘dan takaran 2023 mubaya’a.

Tribune ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, aka ji shugaban shiyyar da wasu mataimakansa su na cewa ba su goyon bayan kowa a zaben Najeriya.

Shugaban kungiyar, Emmanuel Adegboye da mataimakinsa, John Alao da Kakakin kungiyar, Opeoluwa Awoyinfa sun saki jawabi ga manema labarai.

Babu ruwanmu da Tinubu/Shettima Students Vanguard

Kara karanta wannan

Shugaban Yarbawa ya tona asirin Tinubu, ya fadi wata babbar illarsa da yasa ba zai zabe shi ba

A jawabin da aka fitar, kungiyar daliban Najeriyar tace ba ta san da zaman wata Tinubu/Shettima Students Vanguard ko makamancinta a tafiyarta ba.

‘Yan Tinubu/Shettima Students Vanguard ne aka ji suna ikirarin dalliban kasar nan suna tare da tikitin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabannin NANS na Kudu maso yamma sun ce ba su kauce hanyar magabatansu, da za su goyi bayan zalunci da shugabannin da ke mulki suke yi ba.

Bola Tinubu
NANS ta nesanta kanta daga masu goyon bayan Bola Tinubu Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Kafin mu fito da 'dan takaranmu... - NANS

Kungiyar tace ba ta raba kan ta da siyasa, tana sha’awar ganin wa zai karbi mulki a 2023, amma zuwa yanzu ba ta fitar da wanda za a zaba ba tukuna.

A rahoton Vanguard, kungiyar tace tana duba ‘yan takaran shugaban kasa ne domin ganin wanene manfufofinsa za su fi taimakawa dalibai idan ya ci zabe.

Kara karanta wannan

2023: Ɗaliban Najeriya Sun Goyi Bayan Takarar Tinubu Da Shettima, Sun Bada Ƙwakwarar Dalili

Wajen tsaida ‘dan takaran da za a zaba, NANS tace ba za ta nuna kwadayin dukiyar ‘yan siyasa ba, tare da kira ga masu neman mulki su daina kawo rudu.

Wannan karo daliban sun ce ya zama dole su nesanta kansu daga Tinubu/Shettima Students Vanguard, suka ce sam babu abin da ya hada ta da ‘ya ‘yanta.

Kwamred Adegboye da sauran shugabannin NANS suka ce wannan kungiya, hanyar wasu ne a gefe na tatsar kudi daga hannun ‘yan siyasa da sunan dalibai.

Sanatan PDP ya yabi Tinubu

Kun samu rahoto Chimaroke Nnamani wanda ya yi gwamna a Enugu a jam’iyyar PDP tun 1999, babu abin da yake fada a game da Bola Tinubu sai alheri.

An ji Sanata Nnamani yana cewa a lokacin da Tinubu yake gwamna, ya yi zarrra a kan duk sauran abokan aikinsa, saboda ya dauko masu kwakalwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel