2023: Abinda da Yasa Tinubu Zai Lallasa Atiku, Ya Zama Magajin Buhari a 2023, Nkire

2023: Abinda da Yasa Tinubu Zai Lallasa Atiku, Ya Zama Magajin Buhari a 2023, Nkire

  • Jigon APC, Chief Sam Nkire, yace bisa la'akari da rashin zaman lafiya a PDP, Tinubu ba zai sha wahala ba a 2023
  • Mista Nkire yace tarihi ya nuna cewa idan gwamnoni 5 suka yi bore a PDP ba ta kai labari, hakan ke shirin maimaita kansa
  • Ya gargaɗi jam'iyya mai mulki ta gaggauta rarrashin wasu kusoshi da suka fusata don tabbatar da haɗin kan cikin gida

Abuja - Wani jigon jam'iyyar APC na ƙasa, Chief Sam Nkire, yace ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai lashe babban zaben 2023 da ke tafe cikin sauki.

Mista Nkire ya kafa hujjar abinda ya sa ya yi wannan hasahen da ganin alamun gwamnoni 5 na babbar jam'iyyar adawa PDP ka iya janye goyon bayansu ga jam'iyyar.

Bola Ahmed Tinubu
2023: Abinda da Yasa Tinubu Zai Lallasa Atiku, Ya Zama Magajin Buhari a 2023, Nkire Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Nkire, wanda ya kasance tsohon shugaban tawagar yan majalisu na jam'iyyar APC reshen jihar Abiya, ya yi wannan hasashen ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Abuja.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wani Tsohon Gwamna Kuma Babban Jigon PDP Ya Tsame Kansa Daga Kamfen Atiku 2023

A rahoton jaridar Vanguard, Jigon ya haƙaito cewa tarihi na shirin maimaita kansa inda yace, "Duk lokacin da PDP ta rasa goyon bayan gwamnoni biyar ba ta kai labari a zaɓen shugaban ƙasa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abinda ya faru da PDP a 2014 zai maimaita kansa - Nkire

Jigon jam'iyya mai mulkin ya ƙara da cewa a shekarar 2014, jam'iyyar PDP ta rasa gwamnoninta guda biyar kuma ta sha ƙasa a zaɓen 2015 sakamakon faruwar haka.

"Ga dukkan alamu babbar jam'iyyar hamayya PDP ta gaza rarrashin gwamnoni biyar, hakan alamu ne dake nuna APC ta gyara zama a gadon mulki ta hanyar sake samun nasara kan PDP a zaɓe mai zuwa."

Budu da ƙari, Mista Nkire ya gargaɗi jam'iyyarsa cewa ta tashi tsaye ta rarrashi dukkanin mambobin da suka fusata musamman kusoshi masu faɗa a ji.

Kara karanta wannan

Rudani: Gwamnan PDP mai ba Atiku ciwon kai ya zabo tsohon jigon APC ya zama kwamishinansa

A wani labarin kuma Na Kusa da Gwamnan Arewa, Mataimakin Shugaban PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC

Makonni uku bayan fara kamfen 2023, jam'iyyar APC ta kara samun gagarumin goyon baya a jihar Sakkwato.

Hadimin gwamna Aminu Tambuwal da mataimakin shugaban PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da magoya bayansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel