Jigon PDP Ya Cigaba da Tallata Bola Tinubu Duk da Shi Yana Goyon bayan Atiku Abubakar

Jigon PDP Ya Cigaba da Tallata Bola Tinubu Duk da Shi Yana Goyon bayan Atiku Abubakar

  • Chimaroke Nnamani yace a sahun Gwamnonin da aka yi a 1999, babu irin Asiwaju Bola Tinubu
  • Sanata Chimaroke Nnamani yace Bola Tinubu ya samu gagarumar nasara ne saboda aiki da masana
  • ‘Dan siyasar ya saba yabon ‘dan takaran na APC ko da kuwa Atiku Abubakar ne ‘dan takaran PDP

Abuja - Chimaroke Nnamani ya yi gwamnan jihar Enugu ne a karkashin jam’iyyar PDP, amma babu abin da yake fada a game da Bola Tinubu sai alheri.

A ranar Alhamis, The Cable ta rahoto Chimaroke Nnamani yana cewa a lokacin da Bola Tinubu yake gwamna, ya yi zarrra kan duk sauran abokan aikinsa.

Sanata Nnamani yake cewa Tinubu ya tattara gawurtattun masu ilmi, ya yi aiki da su a gwamnatin jihar Legas domin ganin ya kawowa al’ummarsa cigaba.

Kara karanta wannan

‘Dan takaran APC, Tinubu Ya yi karin Haske kan 'tsamin' Alakar Shi da Farfesa Osinbajo

A wani jawabi da ya fitar, ‘dan siyasar yace Tinubu mai neman zama shugaban kasa a yau, ya nemi masana su duba masa duk bangaren da ya shafi jihar.

Daga harkar ilmi zuwa kiwon lafiya, Nnamani yace haka kwararru suka yi nazari na musamman, suka mikawa ‘dan takaran (a lokacin yana Gwamnan jiha).

Bola Tinubu
Tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin Sanata Chimaroke Nnamani

Gwamnonin jihohin da aka yi a shekarar 1999 har gobe sune wadanda suka yi gini, suka kawo sauye-sauye a harkar siyasa.
Mutane da-dama sun manta wahalar da ‘yan sahun 99 suka sha. Kowane bangare ya tabarbare a mafi yawan jihohi a lokacin
Dalili shi ne shekaru barkatai da sojoji suka yi a kan mulki. Abin da ake da shi a lokacin kurum shi ne farin cikin talakawa."

- Sanata Chimaroke Nnamani

Rahoton yake cewa Nnamani yace bayan shekara da shekaru farar hula su na rike da jihohin kasar nan, batun ilmi, tattalin arziki da tsaro sun zama tarihi.

Kara karanta wannan

Gwamna Ortom ya Gindayawa Atiku Abubakar Sharadi 1 na Samun Kuri’un Benuwai

Daga Legas sai Enugu

"Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fi kowa samun nasarori a cikinmu duka wajen kawo sauye-sauye a bangarori da-dama, sai kuma jihar Enugu ta zo ta biyu.
Nasarar da ya samu a dalilin tattara mutane 23 masu tsananin basira a Legas su duba masa kowane bangare, su kawo yadda za a shawo kan irin kalubalensa."

- Sanata Chimaroke Nnamani

Tinubu yana da lafiya - Chimaroke Nnamani

A farkon watan Oktoban nan aka samu rahoto Chimaroke Nnamani ya fitar da jawabi na musamman yana taya Bola Tinubu barka da dawowa daga kasar Ingila.

Tsohon Gwamnan na Enugu ya tabbatar da cewa ‘Dan takaran na jam’iyyar APC bai fama da rashin lafiya, yace ya san hakan domin ya zauna da 'dan siyasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel