‘Dan takaran APC, Tinubu Ya yi karin Haske kan 'tsamin' Alakar Shi da Farfesa Osinbajo

‘Dan takaran APC, Tinubu Ya yi karin Haske kan 'tsamin' Alakar Shi da Farfesa Osinbajo

  • An roki ‘Dan takaran APC a zaben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya yafewa Yemi Osinbajo
  • Magoya bayan Farfesa Yemi Osinbajo sun nemi Bola Tinubu ya rika damawa da ubangidansu
  • Tinubu yace ya yafewa mataimakin shugaban kasar kamar yada yake rokon yafiyar Ubangiji

Kano - Asiwaju Bola Tinubu mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar APC yace babu sabani tsakaninsa da Farfesa Yemi Osinbajo.

Premium Times ta rahoto ‘dan takaran APC watau Asiwaju Bola Tinubu yana cewa bai gaba da tsohon yaron na sa wanda ya yi takarar tikiti da shi.

‘Dan takaran shugaban kasar yace a matsayinsa na mai neman yafiyar Allah, dole ya yafewa mutane.

Bola Tinubu ya yi wannan bayani yayin da yake tattaunawa da wata kungiya da tayi wa Yemi Osinbajo aiki wajen zaben ‘dan takaran shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Gwamna Ortom ya Gindayawa Atiku Abubakar Sharadi 1 na Samun Kuri’un Benuwai

Shugaban kungiyar magoya baya ta Drone Marshall Support Group, Alwan Hassan ya yi kira ga Tinubu ya yi aiki da ‘yan takaran da suka yake shi a APC.

Baya ga Osinbajo akwai irinsu Ahmad Lawan, Rotimi Amaechi da Gwamna Yahaya Bello da suka shiga zaben tsaida gwanin APC, amma ba suyi nasara ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bola Tinubu
Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Alwan Hassan ya fadawa tsohon gwamnan Legas cewa masoya har zuwa makiyansa sun yi masu bayanin irin tsabagen hakurin da yake da shi a siyasa.

A dalilin wannan suka nemi a rika ganin ana dasawa da kyau tsakanin mataimakin shugaban kasa watau Farfesa Osinbajo da Tinubu mai neman takara a 2023.

Ana tare ai - Tinubu

Da ya tashi yin jawabi, Vanguard tace ‘dan siyasar yace ba ya fada da Osinbajo, har ya kai masa ziyara har gida bayan zabe, kuma sun hadu a wajen taron Ministoci.

Kara karanta wannan

Dabarar da Atiku Zai bi, Ya Karbo Kudin da Aka Sace a Najeriya Inji Ologbondiyan

“Mutumin da ke gafara – mai neman Allah ya yi masa gafara yana bukatar ya rika gafara. Idan ba za ka iya yafewa ba, ta ya za ka roki Allah?
A waje na, komai ya zo karshe.” - Bola Tinubu

Atiku yana tsaka-mai-wuya

Dazu an ji labari Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya hada Alhaji Atiku Abubakar da aiki kafin ya mara masa baya a zabe mai zuwa da za ayi.

Mai girma Gwamnan ya yi wa ‘dan takaran kaca-kaca, ya zarge shi da yi masa karya, don haka yace sai ya nemi afuwa kafin mutanen Benuwai su zabe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel