Na Zauna da Tinubu, Jigon PDP Ya yi Bayani a Kan Gaskiyar Lafiyar ‘Dan Takaran APC

Na Zauna da Tinubu, Jigon PDP Ya yi Bayani a Kan Gaskiyar Lafiyar ‘Dan Takaran APC

  • Chimaroke Nnamani ya fitar da jawabi yana mai taya Bola Tinubu barka da dawowa daga kasar Ingila
  • Sanata Chimaroke Nnamani yana cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP, amma yana yawon yabawa Tinubu
  • Tsohon Gwamnan na Enugu ya tabbatar da cewa ‘Dan takaran na jam’iyyar APC bai fama da rashin lafiya

Abuja - Chimaroke Nnamani wanda Sanata ne a karkashin jam’iyyar PDP ya yi magana game da rade-radin da ake yi kan rashin lafiyar Bola Tinubu.

A ranar Litinin da yamma, Tribune ta rahoto Sanata Chimaroke Nnamani yana cewa ya zauna da Bola Tinubu, kuma ya fahimci bai da wata rashin lafiya.

‘Dan siyasar ya fitar da jawabi ga ‘yan jarida a farkon makon nan a garin Abuja, yana ma iyi wa ‘dan takaran na jam’iyyar APC barka da dawowa Najeriya.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023

Tsohon gwamnan na Enugu ya yi fatali da rade-radin da ake yi game da lafiyar Bola Tinubu.

Ina masa barka da zuwa - Nnamani

“Na shiga cikin miliyoyin mutanenmu wajen yi wa Tinubu maraba da dawowa gida. Abin godiya ga Ubangiji ne da ya dawo cikin koshin lafiya.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tinubu
Bola Tinubu wajen taron APC Hoto: @OfficialasiwajuBAT
Asali: Facebook

Ina mai tir da wadanda suke nuna jahilcinsu wajen murnar shirme.
Sai dai ina amfani da murya ta wajen yabawa namijin kokarin da ya yi wajen sha’anin mulki, kawo gyara da bunkasa kananan hukumomi ta kowane fanni.
Ina jinjinawa kwarewar siyasarsa da jajircewarsa.”

- Sanata Chimaroke Nnamani

A matsayinsa na likita, This Day ta rahoto Sanata Nnamani yana bayanin lafiyar tsohon gwamnan na Legas wanda yake takara da jam'iyyarsa.

“Na shaida da kyawun lafiyarsa. Jikin Tinubu yana da kyau sosai, yana ankare da yanayin da ya samu kansa da halin siyasa ta kowace fuska.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

Mutum mai cikakken koshin lafiya da kamala, karfin halinsa a bayyana yake. Zama da shi ya nuna kyawun lafiya, karfi da kuma kazar-kazar.”

- Sanata Chimaroke Nnamani

Nnamani yana tare da APC ne ko PDP?

Kwanaki kun ji labari mataimakin shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo bai samu shiga cikin mutum 422 da za su yi wa Bola Tinubu kamfe ba.

Amma abin mamaki sai ga shi an ga sunan Chimaroke Nnamani wanda 'dan PDP ne. Daga baya jam'iyyar APC tace Sanatan yana yi mata aiki ne a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel