Gwamna Ortom ya Gindayawa Atiku Abubakar Sharadi 1 na Samun Kuri’un Benuwai

Gwamna Ortom ya Gindayawa Atiku Abubakar Sharadi 1 na Samun Kuri’un Benuwai

  • Samuel Ortom ya yi Allah-wadai da wasu kalamai na Atiku Abubakar, yace ‘dan takaran ya yi masa karya
  • Gwamnan jihar Benuwai yace idan Atiku Abubakar bai nemi afuwa ba, mutanensa ba za su zabe shi ba
  • Ortom yace bai yi wa Fulani kudin-goro ba, illa iyaka yana fada ne da Fulanin da ke ta’addanci a Benuwai

Benue - Mai girma Samuel Ortom yace dole ne Alhaji Atiku Abubakar mai neman zama shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya ba mutanen jihar Benuwai hakuri.

Daily Trust ta rahoto Gwamnan na Benuwai a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoba 2022, yana cewa dole Atiku Abubakar ya su hakuri idan yana neman kuri’arsu.

Gwamna Samuel Ortom yace sai ‘dan takaran shugaban kasar ya nemi afuwa a kan karyar da ya yi masa yayin da yake yawon yakin neman takara a Kaduna.

Ortom ya yi wannan kira ne a lokacin da jagororin matasar kabilar Jemgba suka kai masa ziyara a gidan gwamnati a Makurdi suka kai masa karar ‘dan takaran.

Wadannan matasa sun kuma nuna su na tare da takarar Sanatan da Ortom yake yi a 2023.

Jawabin Gwamna Ortom

“Mun yi matukar tir da kalaman da aka yi a kai na. A lokacin da na samu labari, na kokawa shi (Atiku) ta dandalin WhatsApp.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ba ni hakuri, amma ya ki fitowa fili ya fada. Ba za ka girmama babba iri na a fili, sai ka fita waje ka tube mani wando ba.
Atiku a Bayelsa
Atiku Abubakar mai takara a PDP Hoto: @Atiku
Asali: Facebook

Ban taba ba Atiku hakuri, ko na fada masa mutanen Benuwai suna sace mani shanu na ba.

- Samuel Ortom

Tribune ta rahoto Gwamnan yana cewa ba duk Fulani yake suka ba, domin ya ba wasunsu mukami a gwamnati, kuma bai taba korar Bafullatani daga Benuwai ba.

“Ina yaki ne da bakin Fulani ‘yan ta’adda da suke shigowa daga Nijar, Chad, Senagal da Mali.
Dole Atiku ya bada hakuri, ya yi mani karya. Na jinjinawa Buhari da ya yi tir da ta’adin da aka yi a Gbeji, haka ya kamata shugaba ya yi, amma nayi tir da Atiku.

- Samuel Ortom

Muddin ‘dan takaran bai nemi afuwa ba, Gwamnan yace a ranar zabe ba zai ga kuri’unsu ba, yace tun 2017 ake ambaliya a Benuwai, amma Atiku bai taba zuwa ba.

Atiku zai yaki barayi

Kun samu rahoto cewa Atiku Abubakar mai neman takarar shugabancin kasa yana da dabarar takaita matsalar sata da ‘yan siyasa suke tafkawa a kan mulki.

Kakakin kamfe, Kola Ologbondiyan yace ‘dan takaran na 2023 zai yi yadda aka yi da barayin gwamnati a lokacin da Olusegun Obasanjo yake shugabanci a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel