Yabon Peter Obi a Fili Ya Jawo Hadima Ta Rasa Mukami Nan-take a Gwamnatin PDP

Yabon Peter Obi a Fili Ya Jawo Hadima Ta Rasa Mukami Nan-take a Gwamnatin PDP

  • Atare Awin ta rasa mukaminta na Mai taimakawa Kwamishina a Delta saboda tayi maganar siyasa
  • Anthony Onoriode Ofoni ya fatattaki Atare Awin bayan ya ji tana yabon Peter Obi a shafin Facebook
  • Kwamishinan ya yi hakan ne domin nunawa Mai gidansa, Ifeanyi Okowa bai tare da jam’iyyar LP

Delta - Atare Awin ta rasa kujerarta a gwamnatin jihar Delta bayan ta yabi ‘dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party watau Peter Obi.

A karshen makon jiya ne Atare Awin tayi magana a shafinta na Facebook, tana cewa bikin ranar ‘yancin kai ya nuna lallai Peter Obi yana da masoya sosai.

Magoya bayan Obi sun yi gangami a garurwan kasar nan domin tunawa da ranar samun ‘yancin kai da nuna irin farin jini da karbuwar ‘dan takaransu.

Kara karanta wannan

NNPC: Mun Gano Hanyar da Barayi Suka Yi Shekaru 9 Suna Satar Mai Ba a Ankara ba

Jim kadan bayan wannan magana, sai Sahara Reporters ta fitar da rahoto Kwamishinan kula da ayyuka, Anthony Onoriode Ofoni ya kori Atare Awin.

Kafin a sallame ta, Awin tana aiki ne a karkashin ofishin Anthony Onoriode Ofoni a jihar Delta.

Yabon Peter Obi
Atare Awin tana magana a kan soyayyar Peter Obi Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ina mai sanar da ke an sauke ki daga mukamin Mai bada shawara a ofishina na kwamishinan gudanarwa da binciken ayyukan jihar Delta.
Wannan mataki ya zama dole a dalilin yada ra’ayoyinku a game da tsare-tsare da manfofin gwamnatin jihar Delta da kuma na jam'iyyar PDP.
Wanda sun sha bam-bam da nasarorin da gwamnatin jiha ta samu a shekaru bakwai da suka gabata.” - Anthony Onoriode Ofoni.

Ina tare da Gwamna - Kwamishina

A wasikar sallamar, Kwamishinan yace a matsayinsa dole ne ya nesanta kansa daga irin ra’ayoyin Awin, yace yana tare da Mai girma Ifeanyi Arthur Okowa.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Gwamnoni 18 a Najeriya Sun Koma Bayan Takarar Peter Obi a Zaben 2023

Rahoton Daily Post ya nuna Onoriode Ofoni yace Aware za ta bar ofis ba tare da bata lokaci, ya yi mata fatan alheri a inda ta sa gaba ta fuskar ra'ayin siyasa.

Da take magana a Facebook, tsohuwar Hadimar ta godewa masoyanta, ta kuma yi habaici ga mutanen shugaban jam’iyyar PDP da ‘yan majalisar dokoki.

PGF ta sasanta Tinubu, Adamu

Gwamnoni irinsu Atiku Bagudu, Sani Bello, Abubakar Badaru, Oluwarotimi Akeredolu, Abdullahi Sule da Simon Lalong sun dinke barakar APC.

A karshen zamansu, an ji labari ‘Yan majalisar NWC da kuma ‘Yan PCC sun amince za suyi aiki tare domin ganin nasarar takarar Bola Tinubu a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel