NNPC: Mun Gano Hanyar da Barayi Suka Yi Shekaru 9 Suna Satar Mai Ba a Ankara ba

NNPC: Mun Gano Hanyar da Barayi Suka Yi Shekaru 9 Suna Satar Mai Ba a Ankara ba

  • Shugaban Kamfanin man Najeriya, Mele Kolo Kyari ya bayyana a gaban kwamitin hadaka na Majalisa
  • Malam Mele Kolo Kyari ya yi wa ‘Yan majalisa da Sanatoci bayanin yadda ake satar danyen man kasar nan
  • NNPC da Jami’an tsaro sun gano wani bututu da aka kafa daga tasha zuwa teku, ana satar arziki ba a sani ba

Abuja - Kamfanin man Najeriya watau NNPC yace ya gano wata barauniyar hanya da aka yi shekaru kimanin tara ana satar danyen man kasar.

The Cable tace shugaban kamfanin NNPC Limited, Mele Kolo Kyari ya yi wannan bayani ranar Talata yayin da ya je gaban ‘yan majalisar tarayya.

Mele Kolo Kyari ya shaidawa kwamitin harkar mai da gas na majalisar dattawa da na wakilai cewa a kokarin da suke yi an gano barawon bututu.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Ake yi Mani Sharrin Satar $41.8m a lokacin ina Gwamna inji Sanata

Barayi suna amfani da wannan bututu mai tsawon kilomita 4, suna sace danyen mai ta teku.

Ana rasa ganguna 600, 000 duk rana

A jawabinsa, Mele Kyari ya fadawa ‘Yan majalisar wakilan tarayya da Sanatoci cewa gwamnati tana asarar fiye da gangunan mai 600, 000 a kullum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“An yi shekaru fiye da 22 ana satar danyen mai a kasar nan, amma sabon salon da aka dauka a ‘yan kwanakin bayan nan ya zarce na da.
NNPC.
Shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Tashoshin Brass, Forcados, da na Bonny ba su hako komai a yanzu; tasirin wannan shi ne muna asarar ganguna 600, 000 a kowace rana."

- Mele Kolo Kyari

NNPC na kokarin takawa tsageru burki

Reuters ta rahoto shugaban kamfanin NNPCL yana cewa sun hada-kai da jami’an tsaro, suna kokarin maganin masu yi wa tattalin arzikin kasa illa.

A wannan yunkuri da aka yi a makonni shida da suka gabata, Kyari yace sun rufe matatun danyen mai 395 da suke aiki ba tare da an san da zamansu ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: BoT na PDP ta kammala zama da gwamnan da ke ba Atiku ciwon kai

Baya ga haka an ruguza wurare 274 da ake boye mai, sannan an ruguza makamantan tankuna 1561 da manyan motoci 49 da ake amfani da su wajen satar.

Uwa uba, Kyari yace sun rufe wani bututu mai kilomita hudu wanda ya tashi daga tashar Forcados zuwa teku, inda aka yi shekaru tara ana satar mai.

Ayyuka 2000 a shekaru 3

Kun samu labari Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi bayanin irin nasarorin da ya samu a kan kujerarsa.

Farfesa Isa Ibrahim Pantami yace sun yi ayyuka 2000, kuma ya ba mutane shawarar su nemi horon ICT domin samun ayyukan yi a kasashen ketare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel