Babbar Magana: Gwamnoni 18 a Najeriya Sun Koma Bayan Takarar Peter Obi a Zaben 2023

Babbar Magana: Gwamnoni 18 a Najeriya Sun Koma Bayan Takarar Peter Obi a Zaben 2023

  • Gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023, gwamnoni 18 sun koma bayan takarar Peter Obi na jam'iyyar Labour Party
  • Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo ce ta bayyana hakan a cikin wani jawabin manema labarai da ta saki a yau Laraba
  • Babban sakataren kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro, ya ce baya ga gwamnonin akwai wasu manyan tsoffin shugabanni da ke bayan Obi

Ebonyi - Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cewa gwamnoni 18 a fadin jam’iyyun siyasa da kabilu daban-daban suna goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Mista Peter Obi, PM News ta rahoto.

Kungiyar Inyamuran ta bayyana cewa wannan dandali ya zama na yan Najeriya masu muradin ganin an ceto kasar daga mawuyacin hali da take ciki ta bangaren tattalin arziki da zamantakewa.

Kara karanta wannan

Minista ya tona asirin wasu gwamnoni, ya ce suna ba tsageru bindigogi AK-47 a lokacin zabe

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Mazi Okechukwu Isiguzoro, ya gabatarwa manema labarai a ranar Laraba, 5 ga watan Oktoba a Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi.

Peter Obi
Babbar Magana: Gwamnoni 18 a Najeriya Sun Koma Bayan Takarar Peter Obi a Zaben 2023 Hoto: Independent
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa wani bincike da aka gudanar a fadin bangarorin siyasa ya nuna cewa yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa, akwai karin kungiyoyi da ke yin hadaka domin marawa takarar shugabancin Mista Peter Obi baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce baya ga gwamnonin da ba a bayyana sunayensu ba, akwai tsoffin shugabannin kasar nan da ke marawa takarar Obi baya, jaridar Independent ta rahoto.

Ya bayyana cewa gwamnonin sun fito ne daga fadin jam’iyyun siyasa, yana mai cewa tuni APC, PDP, da sauran jam’iyyun siyasa suka tsorata da lamarin.

Kungiyar ta jinjinawa yan Najeriya da suka yi tururuwa daga bangarori daban-daban na kasar don goyawa Peter Obi baya, yana mai cewa dole lamarin ya dore.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: BoT na PDP ta kammala zama da gwamnan da ke ba Atiku ciwon kai

Ya ce:

“Wannan yunkuri ne na mayar da Najeriya zamanin da babu kwadayi, da yan siyasa masu son zuciya.
“Yunkuri ne na ceto Najeriya daga rugujewar tattalin arziki, yajin aikin ASUU, rashin tsaro da cin hanci da rashawa.
“Yan Najeriya sun nuna shirunsu na kwato kasarsu ta akwatin zabe ya kuma rage ga INEC tayi adalci.”

Matashi Ya Zana Katafaren Hoton Peter Obi Jikin Bango A Jihar Kaduna, Yan Najeriya Sun Yi Martani

A wani labarin, wani matashi dan Najeriya da ya shahara wajen yin zanen hotuna iri-iri, Bamaiyi Danladi, ya je shafin intanet don baje kolin wani hadadden aiki da yayi a Kaduna.

A wani bidiyo da ya yadu, matashin ya zana wani katafaren hoton dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a jikin wani bango a jihar.

Ya nuna yadda ya fara zanen har zuwa karshen hoton. Wannan baiwa tasa ta burge yan Najeriya da dama.

Kara karanta wannan

Idan Nayi Nasara Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arziki Kasar, Kwankwaso Ya Yi Alkawari

Asali: Legit.ng

Online view pixel